Da sunan Allah nake maka ruƙya, daga dukkan abinda zai cutar da kai, daga sharrin kowane rai ko maitar mai hassada, Allah Ya warkar da kai, da sunan Allah nake maka ruƙya
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Sa'id - Allah Ya yarda da shi -: Cewa (Mala’ika) Jibril ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Muhammad baka da lafiya ne? sai ya ce: «Eh» ya ce: «Da sunan Allah nake maka ruƙya, daga dukkan abinda zai cutar da kai, daga sharrin kowane rai ko maitar mai hassada, Allah Ya warkar da kai, da sunan Allah nake maka ruƙya».
Explanation
Benefits
Ruƙya tana halatta da sharuɗɗan nan masu zuwa: 1- Ta zama da Alƙur'ani ne ko da ambatan sunan Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma addu'o'in da aka shara'anta. 2- Ta zama da harshen larabci, ko da abinda ake sanin ma'anarsa daga wasu harsunan daban. 3- Ya ƙudirce cewa ruƙya ita akan kanta bata tasiri; kawai ita sababi ce daga cikin sabubban da basa tasiri sai da izinin Allah - Mai girma da ɗaukaka -. 4- Ta kaɗaita daga shirka, ko abinda aka haramta, ko bidi'a, ko abinda zai kai zuwa ga hakan.
Tabbatar da cutar lambing baka ( ko maita), kuma cewa ita gaskiya ce, to yana kamata a nemi yin ruƙya daga gareta.
An so yin ruƙya da abinda ya zo a cikin hadisi.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kamar waninsa ne daga mutane, duk abinda yake samun waninsa na rashin lafiya zai iya samunsa.
Kulawar Allah ga AnnabinSa- tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma kiyayeShi, da wakilta mala'ikunSa da hakan.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

