Haƙƙin musulmi akan musulmi guda shida ne" aka ce: Waɗannene su ya Manzon Allah?, ya ce: "Idan ka haɗu da shi to ka yi masa sallama, idan ya kiraka ka amsa masa, idan ya nemi nasiharka to ka yi masa nasiha, idan ya yi atishawa sai ya godewa Allah to ka gaishe shi, idan ya yi rashin lafiya to ka duba shi, idan ya mutu to kabi shi (ka bi jana'izarsa)
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Haƙƙin musulmi akan musulmi guda shida ne" aka ce: Waɗannene su ya Manzon Allah?, ya ce: "Idan ka haɗu da shi to ka yi masa sallama, idan ya kiraka ka amsa masa, idan ya nemi nasiharka to ka yi masa nasiha, idan ya yi atishawa sai ya godewa Allah to ka gaishe shi, idan ya yi rashin lafiya to ka duba shi, idan ya mutu to kabi shi (ka bi jana'izarsa)".
Explanation
Benefits
Maida sallama farilla ce ta aini idan wanda aka yi wa sallamar shi kaɗai ne, kuma mutum ɗaya ya isarwa jama'a, amma fara sallama to asali a cikinsa shi ne sunnah.
Ziyarar mara lafiya yana daga haƙƙoƙinsa akan 'yan uwansa musulmai; domin cewa ziyara tana shigar da farin ciki da kewa a zuciyarsa, kuma ita farilla ce ta kifaya.
Wajabcin amsa gayyata muddin dai babu wani zunubi a cikinta; idan ta kasance zuwa walimar angwanci ce to jumhur sun tafi akan wajabcin amsata sai dai inda wani uzuri na shari'a, amma idan ta kasance ba walimar angwanci ba ce to jumhur sun tafi a kan cewa sunnah ce.
Gaishe da mai atishawa wajibi ne akan wanda ya ji godiyar (Allah) ga wanda ya yi atishawa ɗin.
Cikar shari'a da kwaɗayinta a cikin ƙarfafa igiyar zamantakewa da imani da alaƙar soyayya tsakanin ɗaiɗaiku.
(Fasammithu) a cikin wasu bugun: (Fashammithu), da Sin mara 'ya'ya da kuma Shin mai 'ya'ya: Addu'a da alheri da kuma albarka, al-Tashmit an ce a cikin ma'anarta: Allah Ya nisantar da kai daga dariyar ƙeta, kuma Ya nisantar da kai abinda maƙiyinka zai yi maka dariyar ƙeta da shi, Tasmit kuma ma'anarsa: Allah Ya shiryar da kai zuwa hanya madaidaiciya.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

