Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan zai yi atishawa, yana sanya hannunsa - ko tufafinsa - a bakinsa, kuma ya runtse - ko matse - muryarsa da shi
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan zai yi atishawa, yana sanya hannunsa - ko tufafinsa - a bakinsa, kuma ya runtse - ko matse - muryarsa da shi.
Explanation
Da farko: Yana ɗora hannunsa, ko tufafinsa akan bakinsa; dan kada wani abu da zai cutar da abokin zamansa ya fita daga bakinsa ko hancinsa.
Na biyu: Yana ƙanƙar da muryarsa ba ya ɗaga ta.
Benefits
An so (mai atishawa ya) ɗora tufafi ko hankici da makancinsa akan bakinsa da hancinsa idan zai yi atishawa, domin kada wani abinda zai cutar da abokin zamansa ya fito daga gare shi.
Kanƙar da murya a atishawa abin so ne, hakan yana daga cikar ladabi, da kuma kyawawan ɗabi'u.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

