Shin kun san mece ce gibah?", suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, sai ya ce: "Ka ambaci ɗan uwanka da abin da yake ƙi
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: "Shin kun san mece ce gibah?", suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, sai ya ce: "Ka ambaci ɗan uwanka da abin da yake ƙi", aka ce: Shin kana ganin in ya kasance akwai abin da nake faɗa a kan ɗan uwana fa? sai ya ce: "Idan ya kasance a cikinsa akwai abin da kake faɗa, to, haƙiƙa ka yi gibarsa, idan babu (abin da kake faɗa) a cikinsa, to, haƙiƙa ka ƙirƙirar masa ƙarya".
Explanation
Amma idan babu siffar a tare da shi, to, wannan ya fi tsanani daga giba, shi ne ƙirƙirar ƙarya, wato: Ƙirkirar abin da babu a tare da shi.
Benefits
Kyakkyawan ladabin sahabbai tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yayin da suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani.
Faɗin wanda aka tamabaya abin da bai sanshi ba; Allah ne mafi sani.
Karewar shari'a ga zamatakewa ta hanyar kare haƙƙoƙi da 'yan uwantaka a tsakaninsu.
Giba abar haramtawa ce sai a wasu halaye dan maslaha; daga hakan akwai: Tunkuɗe zalunci, ta yadda wanda aka zalunta zai ambaci wanda ya zalunceshi ga wanda zai iya karɓa masa haƙƙinsa, sai ya ce: Wane ya zalunceni, ko ya yi min kaza, daga ciki akwai: Shawara a al'amarin aure ko tarayya ko maƙotaka, da makancin hakan.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

