Manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi ya kasance yana bude salla da yin kabbara, da karatu, da fadar Alhamdu lillahi rabbil aalamina, ya kasance idan yayi ruku`u baya dago kansa, baya kuma mikar da shi saidai tsaka tsaki
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
An karbo daga A`isha -Allah ya kara yarda a gareta- ta ce: Manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi ya kasance {yana bude salla da kabbara. da karatu, da fadar Alhamdu lillahi rabbil aalamina, ya kasance idan yayi ruku`u baya dago kansa, ba kuma ya mikar da shi saidai tsaka tsaki, ya kasance idan ya dago kansa daga ruku`i baya yin sujjada, har sai ya daidaita a tsaye, ya kuma kasance idan ya dago kansa daga sujjada, baya kuma sujjada har sai ya daidaita a zaune, ya kasance yana yin tahiya a bayan kowace raka`a biyu, ya kasance yana shimfida kafar sa ta hagu ya kuma kafe kafar sa ta dama, ya kasance yana yin hani gameda irin zaman shaidan. sa`annan yana yin hani mutum ya shimfida hannayen sa guda biyu irin shimfidawar zaki, ya kasance yana rufe sallar da yin sallama}.
Explanation
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

