Wanda ya ci tafarnuwa ko albasa, to ya yi nesa damu - ko cewa ya yi: Ya yi nesa da - masallacinmu, ya zauna a gidansa
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya ci tafarnuwa ko albasa, to ya yi nesa damu - ko cewa ya yi: Ya yi nesa da - masallacinmu, ya zauna a gidansa", kuma cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - an zo masa da wata tukunya a cikinta akwai korren abubuwa daga maɓungura ƙasa, sai ya ji wari daga gareta, sai ya yi tambaya sai aka ba shi labarin abinda ke cikinta na maɓungura ƙasa, sai ya ce ku kusantar da ita ga wani daga sahabbaina wanda ke tare da shi, lokacin da ya ganta sai ya ƙyamaci cinta, ya ce: "Ka ci domin cewa ni ina ganawa da wanda ba ka ganawa (da shi)". A riyawayar Muslim daga Jabir ɗan Abdullahi, daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wanda ya ci daga waɗannan maɓungura ƙasan, tafarnuwa - wani lokacin kuma ya ce: Wanda ya ci albasa da tafarnuwa da algarif to kada ya kusanci masallacinmu, domin mala'iku suna cutuwa da abinda 'ya'yan Adam suke cutuwa da shi".
Explanation
kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mala'iku suna cutuwa daga warin da ake ƙi, kamar yadda mutane suke cutuwa daga gare shi.
Benefits
Ana riskar da waɗannan abubuwan, dukkan abinda yake da warin da masallata suke cutuwa daga gare shi, kamar warin taba da wiwi da makancin hakan.
Illar hanin “wari”, idan ya gushe da yawan dafuwa ko wanin hakan; to karhancin ya gushe.
Karhancin cin waɗannan abubuwan ga wanda zuwa sallah a masallaci ya wajaba akansa; dan kada jam'i ya wuce shi a cikin masallaci, muddin dai bai ci ba dan dabara akan kin halarta, to (cin) ya haramta.
Hanuwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga cin tafarnuwa da makancinsa, badan haramcinsa ba ne, kawai dan ganawarsa ne da (mala'ika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi -.
Kyakkyawan koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda yake haɗa hukunci da bayanin sababinsa; dan wanda ake magana ya nutsu da sanin hikimar.
Alkali ya ce: Malamai sun ƙiyasta wanin masallaci akan wuraren haɗuwa dan yin sallah, kamar wurin sallar idi da jana'iza da makancinsu daga wuraren taruwa dan yin ibadu, haka nan wuraren taruwa na ilimi da zikiri da walimomi da makancinsu, ba za'a riskar da kasuwanni da wasunsu da su ba.
Malamai sun ce: A cikin wannan hadisin akwai dalili akan hana cin tafarnuwa da makamancinta daga shiga masallaci - koda ya kasance ba kowa - domin shi guri ne na mala'iku, kuma saboda gamewar hadisan.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

