Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Agar - Allah Ya yarda da shi -, kuma ya kasance daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: Manzon Allah - tsiar da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari".
Explanation
Benefits
Tuba a game daidai ne daga aikata abubuwan da aka haramta ne da zunubai ko daga kasawa ne a aikata wajibai.
Ikhlasi a cikin tuba sharaɗi ne akan karbar tuban, wanda ya bar wani zunubi ba dan Allah ba to ba ya kasancewa mai tuba.
AlNawawi ya ce: A kwai sharuɗɗa uku ga tuba: Ya bar aikata saɓo, kuma ya yi nadama akan aikata shi, kuma ya ƙudirci niyya a yanke cewa ba zai koma ba zuwa tamkarta ba har abada, idan saɓon yana rataye ne da ɗan Adam to yana da sharaɗi na huɗu, shi ne: Maida abinda aka zalinta zuwa ga mai shi, ko tabbatar da kuɓuta daga gare shi.
Faɗakarwa akan neman gafarar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ya lazimtar cewa ya kasance dan wasu zunuban da ya aikata su ne, sai dai hakan dan cikar ubudiyyarsa ne da kuma danfaruwa da ambatanSa - tsarki ya tabbatar maSa - da jinsa girman haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki - da kasawar bawa duk aikin da ya aikata a godiyar ni'imominSa, hakan yana daga babin shara'antawa ga al'umma a bayansa ne, zuwa wanin hakan daga hikimomi.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

