Kwatankwacin abinda Allah Ya aikoni da shi, na shiriya da ilimi kamar kwatankwacin girgije ne mai yawa da ya zuba a wata ƙasa
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Kwatankwacin abinda Allah Ya aikoni da shi, na shiriya da ilimi kamar kwatankwacin girgije ne mai yawa da ya zuba a wata ƙasa, daga cikinta akwai tsarkakakkiya, ta karɓi ruwa, sai ta tsirar da ciyawa mai yawa, kuma daga cikinta akwai mai fari, ta riƙe ruwan, sai Allah Ya amfani mutane da ita, sai suka sha suka shayar, kuma suka yi shuka, kuma ruwan ya samu wani ɓangare daban, wanda shi kawai faƙo ne ba ya riƙe ruwan kuma ba ya tsirar da ciyawa, to hakan kwatankwacin wanda ya fahimci Addinin Allah ne kuma Ya amfanar da shi da abinda Allah Ya aikoni da shi, sai ya sani ya kuma sanar, da kwatankwacin wanda bai ɗaga kai ba da hakan, kuma bai karɓi shiriyar Allah ba wacce aka aikoni da ita ba».
Explanation
Benefits
Buga misalai dan kusanto da ma'anoni ga mutane.
AlƘurɗubi ya ce: Kamar yadda cewa girgije yana raya mataccen gari haka nan ilimummukan Addini suna raya matacciyar zuciya, sannan ya kamanta masu jinsa da ƙasa mai banbancin abinda girgijen yake saukar wa na ruwa a kanta.
Mutane matakai ne a karɓar ilimin shari'a.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

