Haƙiƙa kin faɗi kalmar da za'a cakuɗata da ruwan kogi da ta canza shi
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya isheka abu kaza da abu kaza daga Safiyya, - wani daga maruwaita ya ce: Tana nufin cewa ita gajera ce - sai ya ce: «Haƙiƙa kin faɗi kalmar da za'a cakuɗata da ruwan kogi da ta canza shi» ta ce: Kuma na kwaikwayi wani mutum gare shi , sai ya ce: «Bana son ace na kwaikwayi wani mutum koda kuwa (na karɓi) abu kaza da abu kaza».
Explanation
Benefits
Kwaikwayar yanayi da kwaikwayon mutane ta hanyar wulaƙantarwa da tauyewa yana daga yi da mutum wanda yake haramun ne.
Siffanta aibuka na jiki wani yanki ne na yi da mutum.
Alƙali ya ce: al-Mazju shi ne cakuɗawa da kuma canjawa ta hanyar cakuɗa waninsa da shi, ma'ana cewa wannan gibar da ace ta zama daga abinda za'a cakuɗa da ruwan kogi da ta canja shi daga yadda yake, duk da yawansa, to yaya kuwa da ace ayyuka ne kaɗan suka cakuɗa da shi.
Bayanin abin da yake faruwa tsakanin ma'aurata na kishi.
Rashin tabbatarwarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga wani aiki abin ƙi.
Wulaƙantar da sha'anin duniya da abinda ke cikinta idan an haɗa da yardar Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma rashin fushinSa.
Musulunci Addini ne na ɗabi'u masu kyau, haƙiƙa an yi umarni da kiyaye mutunci kada a keta shi da magana ne ko da aiki; domin cewa shi yana daga abinda yake gadar da gaba da ƙiyayya tsakaknin musulmai.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

