Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Assalamu alaikum (Aminci ya tabbata agare ku), sai ya amsa masa sannan ya zauna, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Goma
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Imran ɗan Husain - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Assalamu alaikum (Aminci ya tabbata agare ku), sai ya amsa masa sannan ya zauna, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Goma» Sannan wani ya zo sai ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai ya ce: «Ashirin», sannan wani ya zo sai ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai ya ce: «Talatin».
Explanation
Benefits
Karin lada (yana kasancewa ne) da ƙarin lafazan sallama.
Mafi cika a yin sallama: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), kuma mafificiyar siga a amsa (sallama): Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh (Kuma aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa).
Matakan sallama da amsawa masu wuce juna ne ladan ma haka.
Koyawa mutane alheri da kuma faɗakar da su akan samun abinda ya fi.
Ibnu Hajar ya ce: Da ace mai fara (sallama) zai ƙara (da rahamar Allah) an so a ƙara (da albarkarSa), da ace zai ƙara (da albarkarSa) shin a shara'anta ƙari a cikin amsawar? haka nan da ace mai fara (sallama) ya yi ƙari akan (da albarkarSa) shin an shara'anta masa hakan, (Imam) Malik ya fitar a cikin Muwaɗɗa daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Sallama tana ƙarewa ne zuwa albarka.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

