Ku tashi wallahi ni zanyi muku Sallah
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
An karbo daga Anas Dan Malik Allah ya yarda dashi"Cewa Kakarsa Mulaika ta gaiyaci Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi saboda wani Abinci da ta shirya masa,sai yaci daga gareshi.sannan yace:ku tashi nai muku Salla?sai Anas yace:Sai na tashi zuwa wata Tabarmarmu wace tayi Kura saboda an dade da shinfida ta,sai na yayyafa mata Ruwa,sai Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya tsaya akanta ni da Marayan sai muka yi sahu a bayansa,Tsohuwar kuma tana daga bayanmu, sai yayi mana Salla raka'a Biyu sannan ya juya".Daga Muslim kuma"Cewa Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi masa Salla da Mahaifiyarsa sai ya tsayar dani a Damansa,ya tsayar da Macen a bayanmu".
Explanation
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

