Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa , babu wani daya daga wannan al'ummar da zai ji ni Bayahude ne ko Kirista, sannan ya mutu bai yi imani da abinda aka aikoni da shi ba sai ya zama cikin 'yan wuta
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa , babu wani daya daga wannan al'ummar da zai ji ni Bayahude ne ko Kirista, sannan ya mutu bai yi imani da abinda aka aikoni da shi ba sai ya zama cikin 'yan wuta".
Explanation
Benefits
Wanda ya kafirce da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata aagre shi - ikirarins na imani da waninsa daga Annabawa - tsira da aminci ya tabbata agare su baki daya - ba zai amfanar da shi da komai ba.
Wanda bai ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba, kuma sakon musulunci bai isa zuwa gare shi ba to shi yana da uzuri, al'amarinsa a lahira yana ga Allah - Madaukakin sarki -.
Amfanuwa da musulunci yana tabbata koda kafin mutuwa ne, koda a halin tsananin rashin lafiya ne, muddin dai rai bai kai makogwaro ba.
Inganta Addinin kafirai - daga cikinsu akwai yahudawa da kiristoci - kafirci ne.
Ambaton yahudawa da kiristoci - a cikin hadisin - dan fadakarwa ne akan wasunsu; hakan domin cewa yahudawa da kiristoci suna da littafi, idan hakan ya zama sha'aninsu, to wasunsu daga wadanda ba su da littafi ya fi cancanta, dukkaninsu shiga Addininsa da biyayya gareshi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zama dole akansu.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

