Koma ka yi sallah domin cewa kai baka yi sallah ba
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -ya shiga masallaci, sai wani mutum ya shigo, sai ya yi sallah, sannan (ya zo) ya yi sallama ga Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi-sai ya amsa masa kuma ya ce: Koma ka yi sallah domin cewa kai baka yi sallah ba", sai ya koma ya yi sallah kamar yadda ya yi sallar, sannan ya zo ya yi sallama ga-Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: "Koma ka yi sallah, domin cewa kai baka yi sallah ba" sau uku, sai ya ce: Na rantse da wanda ya aikoka da gaskiya ba zan iya yin wacce ta fita ba, to ka koya mini, sai ya ce:
"Idan ka tashi zuwa sallah to ka yi kabbara, sannan ka karanta abinda ya sawwaka tare da kai na Alkur'ani, sannan ka yi ruku'u har sai ka natsu kana mai ruku'u, sannan ka dago har sai ka daidaita a tsaye, sannan ka yi sujjada har sai ka natsu kana mai sujjada, sannan ka dago har sai ka natsu a zaune, kuma ka aikata hakan acikin sallarka gaba dayanta".
Explanation
Benefits
Natsuwa rukuni ce daga cikin rukunan sallah.
Nawawi ya ce: A cikinsa cewa wanda ya ɓata wasu wajiban sallah to sallarsa ba ta inganta ba.
Nawawi ya ce: Kuma a cikinsa akwai sauƙaƙawa ga mai neman sani da kuma jahili da sassauta masa, da bayyanar da masa'alar gare shi da rairaye manufofi, da taƙaitawa a matakinsa akan manyan mihimmai banda wadanda suke cikawa waɗanda halinsa ba zai iya ɗaukar iya kiyayesu da kuma tsayuwa da su ba.
Nawawi ya ce: Kuma a cikinsa cewa mai bada fatawa idan an tambaye shi game da wani abu, kuma a nan akwai wani abu daban da mai tambayar yake buƙatuwa zuwa gare shi kuma bai tambaye shi ba to an so ga matawar ya faɗa masa shi, kuma wannan ya zama daga nasiha ne ba daga zancen da bai shafe shi ba ne.
Falalar iƙirari da kasawa saboda faɗinsa; "Ba zan iya yin wacce ta fi ta ba to ka koya mini".
Ibnu Hajar ya ce: Kuma a cikinsa akwai horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ƙi, da kuma neman mai neman sani daga malami cewa ya koya masa.
An so yin sallama a lokacin haɗuwa, da kuma wajabcin amsa ta, kuma an so maimaitata idan haɗuwa ta maimaitu koda ba'ajima ba, kuma cewa wajibi ne ya amsa masa a kowane lokaci.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

