Ki ɗauki abin da zai ishe ki ke da 'ya'yanki daga cikin dukiyarsa ba tare da barna ba
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Hindu 'yar Utbatah - matar Abu Sufyan- ta shigo wajen Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sai ta ce:
Ya Manzon Allah, Abu Sufyan ya kasance mutum ne mai ƙwauro, ba ya bamu abin da zai ishe mu ni da 'ya'ya na sai abinda na ɗauka daga cikin dukiyarsa ba tare da saninsa ba, shin ba laifi akaina a yin hakan? Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ki ɗauki abin da zai ishe ki ke da 'ya'yanki daga cikin dukiyarsa ba tare da barna ba".
Explanation
Benefits
Ibnu Hajar ya ce: Abin nufi a faɗinsa: "Ki ɗauki abinda zai isheki cikin dukiyarsa ta yadda al'ada take gudana da shi", sai ya mayar da ita zuwa ga al'ada a cikin abinda babu iyakancewar shari'a a cikinsa.
Ibnu Hajar ya ce: An kafa hujja da wanna hadisin akan halaccin ambatan mutum da abinda ba ya ƙayatar da shi idan ya kasance ta fuskar neman fatawa ne da kai ƙara da makamancin haka, kuma shi ne ɗaya daga cikin guraren da aka halatta giba (yi da mutum) a cikinsu.
AlƘurɗubi ya ce: Hindu bata nufin siffanta Abu Sufyan da ƙwauro a dukkanin halayensa, kawai ta siffanta halinta ne tare da shi kuma cewa shi yana yi mata ƙwauro ita da 'ya'yanta, wannan ba ya lazimtar rowa kai tsaye, domin cewa mafi yawancin shugabanni sunayin haka tare da iyalansu suna fifita na waje dan jawo zukatansu.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

