Sallar jam'i ta fi sallar ɗayanku shi kaɗai, da yanki ashirin da biyar, kuma mala'ikun dare da mala'ikun rana suna taruwa a sallar Asuba
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Sallar jam'i ta fi sallar ɗayanku shi kaɗai, da yanki ashirin da biyar, kuma mala'ikun dare da mala'ikun rana suna taruwa a sallar Asuba" Sannan Abu Huraira ya ce: Idan kun so ku karanta: {Lallai karatun alfijir (sallar Asuba) ya kasance abin halartowar (mala'iku) ne} [al-Isra'i: 78].
Explanation
Idan kun so ku karanta: {Lallai karatun alfijir (sallar Asuba) ya kasance abin halartar (mala'iku) ne} [al-Isra'a: 78]. Wato: Lallai sallar Asuba mala'ikun dare da mala'ikun rana suna halartarta.
Benefits
A cikinsa akwai falalar sallar Asuba; dan keɓantuwar mala'iku da ita.
Ibnu Baaz ya ce: Yana kamata ga mumini ya yi kwaɗayin kiyaye sallah a cikin jama'a koda gidansa ya yi nisa dan ya samu wannan alherin mai girma.
Nawawi ya faɗa a akan haɗa wadannan ruwayoyin cewa sallar jama'a ta fi sallar mutum ɗaya da daraja ashirin da biyar, ɗaya riwayar kuma da ashirin da bakwai: Haɗawa tsakaninsu ta fuskoki uku ne: Ta farkonsu: Cewa babu korewa (tsakaninsu), ambatan kaɗan ba ya kore mai yawa, kuma mafhumul adadi ɓatacce ne a wurin malaman Usulul Fiƙhi. Na biyu: Ta zama tun farko ya labarta kaɗan ɗin, sannan Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanar da shi ƙarin falala, sai ya bayar da bayaninta. Na uku: Cewa shi ya banbanta a tsakanin yanayin masallata da kuma sallar, sai ta zama ashirin da biyar ga wasunsu, ga wasunsu kuma ashirin da bakwai gwargwadan cikar sallar da kuma kiyayewarsa akan siffarta da kushu'inta da yawan jama'arta da falalarsu da kuma darajar wurin (sallar) da makamancin hakan. Allah ne Mafi sani.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

