Na yi sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya kasance yana yin sallama a damansa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa", kuma a hagunsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Wa'il ɗan Hujur - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na yi sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya kasance yana yin sallama a damansa:
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
"Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa", kuma a hagunsa:
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
"Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah".
Explanation
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
(Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), kuma yana yin sallama a hagunsa, shi ne ya juyar da fuskarsa ɓangaren hagu, tare da faɗinsa:
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
(Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah).
Benefits
An so zuwa da ƙarin faɗin: (Da albarkarSa), a sashin lokuta; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance yana dawwama akanta ba.
Furta sallama biyu a cikin sallah rukuni ne na wajibi, amma yin waiwaye a tsakiyar furta su to (Mustahabbi ne) abin so ne.
Yana kamata ya ce: (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah) a tsakiyar yin waiwaye ba kafinsa ko bayansa ba.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

