An umarceni in yi sujjada akan gabbai bakwai
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "An umarceni in yi sujjada akan gabbai bakwai: Akan goshi sai ya yi nuni da hannunsa akan hancinsa, da hannaye, da gwiwoyi, da gefunan diga-digai, kuma kada ka tufke tufafi ko gashi".
Explanation
Na farko: Goshi: Shi ne: Fatar fuska a saman hanci da idanuwa, Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi nuni zuwa hancinsa, yana mai bayyana cewa goshi da hanci gaba daya ce daga bakwan, da kuma karfafa cewa mai sujjada yana shafar kasa da hancinsa.
Gaba ta biyu da ta uku: Hannaye.
Ta hudu da ta biyar: Gwiwoyi.
ta shida da ta bakwai: 'Yan yatsun diga-digai.
Kuma ya umarcemu kada mu daure gashin mu, ko mu tattaro tufafinmu sashinsu akan sashi a yayin sujjada akan kasa dan karesu; kai ya sake su har su sauka a kasa, sai ka yi sujjada tare da gabbai.
Benefits
Karhancin tattaro tufafi da gashi a cikin sallah.
Yana wajaba akan mai sallah ya natsu a cikin sallarsa, hakan ya sanya gabban sujjada guda bakwai akan kasa, ya tabbata akansu har ya zo da zikirin da aka shara'anta.
Hani daga kame gashi (wannan) ya kebanci maza banda mata; domin cewa mace a cikin sallah abar umarta ce da sutaurtawa.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

