Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana buɗe sallah da kabbara, da kuma karatu, da (faɗar) Alhamdu lillahi rabbil aalamina (Dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai)
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana buɗe sallah da kabbara, da kuma karatu, da (faɗar) Alhamdu lillahi rabbil aalamina (Dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai), ya kasance idan ya yi ruku`u ba ya ɗago kansa, ba kuma ya miƙar da shi saidai tsaka-tsaki, ya kasance idan ya ɗago kansa daga ruku`i ba ya yin sujjada, har sai ya daidaita a tsaye, ya kuma kasance idan ya ɗago kansa daga sujjada, ba ya kuma sujjada har sai ya daidaita a zaune, ya kasance yana yin tahiya a bayan kowace raka`a biyu, ya kasance yana shimfiɗa ƙafar sa ta hagu ya kuma kafe ƙafar sa ta dama, ya kasance yana yin hani gameda irin zaman shaiɗan. sannan yana yin hani mutum ya shimfiɗa hannayen sa guda biyu irin shimfiɗawar namun daji, ya kasance yana rufe sallar da yin sallama.
Explanation
Benefits
Wajabcin kabbarar haramar da take haramta kowace magana da aikin da yake kore maganganun sallah da kuma ayyukanta, kuma wanin wannan sigar (ta Allahu Akbar) ba ta tsayawa matsayinsu dan shiga cikin sallah.
Wajabcin karatun Fatiha.
Wajabcin ruku'u, abin da ya fi a cikinsa shi ne daidaituwa ba tare da ɗagawa, ko sunkuyarwa ba.
Wajabcin ɗagowa daga ruku'u, da kuma wajabcin daidaituwa a cikin tsayuwa a bayansa.
Wajabcin sujjada, da wajabcin ɗagowa daga gareta, da kuma daidaituwa a zaune a bayanta.
Halaccin mai sallah ya shimfiɗa ƙafarsa ta hagu da kafa ta dama a lokacin zama a cikin sallah, amma a cikin tahiyar ƙarshe a cikin sallar da a cikinta akwai tahiyoyi biyu kamar magariba da issha'i to abin da aka shara'anta shine tawarruk, haƙiƙa hadisai da yawa sun zo da hakan.
Hani daga kamanceceniya da shaiɗan a zamansa, hakan shi ne ya zauna akan ƙarshen ƙafafuwansa ya shimfiɗa ƙafafuwansa akan ƙasa, ko ya kafasu ya zauna a tsakaninsu akan ƙasa.
Hani daga kamanceceniya da namun daji a yadda suke shimfiɗa ƙafafuwansu, hakan shi ne mai sallah ya shimfiɗa zira'insa a ƙasa, domin hakan alama ce ta kasala da rauni.
Hani daga kamanceceniya da shaiɗan da kuma dabbobi a cikin ayyukan sallah.
Wajabcin rufe sallah da yin sallama, shi ne yi wa masu sallah mahalarta da waɗanda basa nan, amma salihai addu'a da kuɓuta daga dukkanin sharri.
Wajabcin nutsuwa a cikin sallah.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

