Lokuta uku Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana hana mu yin salla a cikinsu, ko binne mamatanmu a cikinsu
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Uƙuba ɗan Amir al-Juhani - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Lokuta uku Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana hana mu yin salla a cikinsu, ko binne mamatanmu a cikinsu:
Lokacin da rana ta fito a bayyane har sai ta ɗaga, da kuma lokacin da ta tsaya a tsakiyar sama har sai ranar ta karkace, da kuma lokacin da ranar ta kusa faɗuwa har sai ta faɗi.
Explanation
Benefits
Hani akan yin sallah a waɗannan lokutan guda biyar waɗanda aka yi hani a cikinsu, an togance farillai da (salloli) masu sabubba daga hanin.
Hani daga jinkirta binne (mamaci) da gangan zuwa waɗannan lokutan guda uku ƙuntatattu waɗanda aka ambata a cikin hadisin, da kuma halaccinsa a cikin kowanne lokaci na dare ko na rana.
Hikima akan hana sallah a cikin waɗannan lokutan: Asali musulmi ya miƙa wuya ga dukkanin umarnin Allah, kuma ya nisanci hane-hanenSa dan yin bauta ga Allah, kada ya tsaya daga bauta har sai ya tsinkayi hikima ko illa daga umarni kaza, ko hani akan hakan, kawai ya wajaba a kansa ya miƙa wuya, haƙiƙa wasu hikimomin sun zo ne a cikin wasu hadisan daban a cikin hakan: Na farko: Lallai cewa a lokacin garjin azahar, kafin zawali ana kunna wuta ta Jahannama kunnawa mai kaiwa koli. Na biyu: Hikima akan hani daga yin sallah a lokacin ɓullowar rana da lokacin faɗuwarta, don hakan kamanceceniya ce da mushrikai, domin su suna yi wa rana sujjada a lokacin bullowarta da lokacin faduwarta. Na uku: Amma hani akan sallah bayan sallar Asuba zuwa bullowar rana, da bayan sallar La'asar har zuwa faduwar rana, to dan toshe kafa ne; don kamanceceniya da kafirai ya yanke, kuma kada musulmi ya yi kamanceceniya da su a cikin shirkarsu, domin cewa su suna yin sujjada ga rana a lokacin bullowarta da lokacin faɗuwarta.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

