*Yaushe ake karanta ayatul Kursiyyu?*
1- *Bayan Sallolin farillah biyar;*
Manzon Allah -Sallallahu Alaihi wasallam- ya ce:
" *Duk wanda ya karanta ayatul Kursiyyu a bayan kowace Sallah ta farillah, babu abin da zai hanashi shiga Aljannah se mutuwa*".
2- *Kafin a kwanta barci;*
Ya tabbata a hadisi cewa: ( *duk wanda ya karanta ayatul Kursiyyu kafin ya kwanta barci to wani mai gadi bazai gusheba yana gadinsa, kuma Shaidan bazai kusanceshi ba har ya wayi gari*).
Ayatul Kursiyyu itace Aya mafi girma a cikin littafin Allah, kamar yanda Annabi -sallallahu Alaihi wasallam- ya fada.
Tashar yara
Koyon karatu tareda wasa kwakwalwa karkashin kulawar: Shaikh Haitham Sarhan.