
KUMA INA RANTSUWA DA DARARE GOMA Wato dadare goman farkon watan Zulhijjah Da wane ayyuka za mu fuskanci waɗannan kwanakin?
KUMA INA RANTSUWA DA DARARE GOMA Wato dadare goman farkon watan Zulhijjah وليالٍ عشر ليالي ذي الحجة Da wane ayyuka za mu fuskanci waɗannan kwanakin? Hadisi ya zo daga Abdullahi ɗan Abbas RA, ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Babu wasu kwanaki waɗanda Sallah Mabuwayi da ɗaukaka yafi son ayyukan kirki a cikinsu fiye da waɗannan kwanakin? (Wato, yinin nan guda goma). Suka ce: Ya Manzon Allah, koda jihadi ne fiysabilil Lah? Ya ce: koda jihadi ne fiysabilil Lahi; saidai ga mutumin...
KUMA INA RANTSUWA DA DARARE GOMA Wato dadare goman farkon watan Zulhijjah Da wane ayyuka za mu fuskanci waɗannan kwanakin?
KUMA INA RANTSUWA DA DARARE GOMA
Wato dadare goman farkon watan Zulhijjah
وليالٍ عشر
ليالي ذي الحجة
Da wane ayyuka za mu fuskanci waɗannan kwanakin?
Hadisi ya zo daga Abdullahi ɗan Abbas RA, ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Babu wasu kwanaki waɗanda Sallah Mabuwayi da ɗaukaka yafi son ayyukan kirki a cikinsu fiye da waɗannan kwanakin? (Wato, yinin nan guda goma). Suka ce: Ya Manzon Allah, koda jihadi ne fiysabilil Lah? Ya ce: koda jihadi ne fiysabilil Lahi; saidai ga mutumin da ya fita da kansa da dukiyarsa, sai bai komo da komai ba.
Shi kuma aikin kwarai da aka ambata, ya game dukkan nau'ukan ibada; kamar azumi da salla da hajji da zikiri, da kabbara domin girmama Allah Ta'alah, da karayun Alƙur'ani, da ciyar da dukiya a fuskokin ayyukan biyayya, da makamancin haka.
Kuma yana daga abinda ake ƙarfafawa a cikin waɗannan kwanakin:
1- YIN AZUMINSU, in banda ranar goma (ranar layya), saboda hadisi ya zo daga wata daga cikin matan Manzon Allah SAW lallai ta ce: MANZON ALLAH SAW ya kasance yana yin azumin kwanaki taran Zulhijjah. Musamman yin azumin ranar Arafah, wanda azumtarsa yake kankare zunubin shekaru biyu.
2- YIN HAJJI: Kuma shine mafificin aikin da aka aikata shi a cikin kwanakin nan goma, Annabi SAW ya ce: Hajji lafiyayye bashi da wani sakamako face Aljannah.
3- YIN LAYYA: sunna ne mai ƙarfi, kuma duk wanda ya yi nufin ya yi layya, to sai ya kame daga aske gashinsa, da yanke farcensa, tun daga shigan watan Zulhijjah, har sai bayan ya yanka abar layyarsa.
4- YAWAITA YIN Hailala da kabbara da hamdala (zikiri), kuma sifar kabbarar ita ce: Faɗin ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILA ILLAL LAHU, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LIL LAHIL HAMDU.
File | Action |
---|---|
photo_٢٠٢٤-٠٦-٠٧_١٧-٢٨-٣٣.jpg | Download |

KUMA INA RANTSUWA DA DARARE GOMA Wato dadare goman farkon watan Zulhijjah Da wane ayyuka za mu fuskanci waɗannan kwanakin?
Scan QR Code | Use a QR Code Scanner to fast download directly to your mobile device

( وماهو على الغيب بضنين ) viņš nav skops attiecībā uz atklāsmi, nedz arī slinko vēstījuma nodošanā un mācīšanā, bet gan sniedz visas zināšanas, kuras cilvēks ir gatavs saņemt, atšķirībā no zīlniekiem." Zīlnieki neko nedod, nemāca un nesniedz zināšanas, kuras apgalvo zinām, izņemot par samaksu.
April 22, 2025