المطففين

 

Al-Mutaffifin

 

The Defrauding

1 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 001

وَيۡلٞ لِّلۡمُطَفِّفِينَ
Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.

2 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 002

ٱلَّذِينَ إِذَا ٱكۡتَالُواْ عَلَى ٱلنَّاسِ يَسۡتَوۡفُونَ
Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.

3 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 003

وَإِذَا كَالُوهُمۡ أَو وَّزَنُوهُمۡ يُخۡسِرُونَ
Kuma idan sun auna musu da zakka* ko da sikẽli, suna ragẽwa
* Mũdu.

4 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 004

أَلَا يَظُنُّ أُوْلَـٰٓئِكَ أَنَّهُم مَّبۡعُوثُونَ
Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?

5 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 005

لِيَوۡمٍ عَظِيمٖ
Domin yini mai girma.

6 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 006

يَوۡمَ يَقُومُ ٱلنَّاسُ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?

7 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 007

كَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلۡفُجَّارِ لَفِي سِجِّينٖ
Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.

8 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 008

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا سِجِّينٞ
Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?

9 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 009

كِتَٰبٞ مَّرۡقُومٞ
Wani ittãfi ne rubũtacce.

10 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 010

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.

11 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 011

ٱلَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوۡمِ ٱلدِّينِ
Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.

12 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 012

وَمَا يُكَذِّبُ بِهِۦٓ إِلَّا كُلُّ مُعۡتَدٍ أَثِيمٍ
Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.

13 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 013

إِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِ ءَايَٰتُنَا قَالَ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.

14 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 014

كَلَّاۖ بَلۡۜ رَانَ عَلَىٰ قُلُوبِهِم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.

15 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 015

كَلَّآ إِنَّهُمۡ عَن رَّبِّهِمۡ يَوۡمَئِذٖ لَّمَحۡجُوبُونَ
A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.

16 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 016

ثُمَّ إِنَّهُمۡ لَصَالُواْ ٱلۡجَحِيمِ
Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.

17 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 017

ثُمَّ يُقَالُ هَٰذَا ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ
Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi."

18 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 018

كَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلۡأَبۡرَارِ لَفِي عِلِّيِّينَ
A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna?

19 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 019

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا عِلِّيُّونَ
Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?

20 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 020

كِتَٰبٞ مَّرۡقُومٞ
Wani littãfi ne rubũtacce.

21 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 021

يَشۡهَدُهُ ٱلۡمُقَرَّبُونَ
Muƙarrabai* suke halarta shi.
* Malã'iku masu daraja.

22 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 022

إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ لَفِي نَعِيمٍ
Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.

23 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 023

عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ
A kan karagu, suna ta kallo.

24 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 024

تَعۡرِفُ فِي وُجُوهِهِمۡ نَضۡرَةَ ٱلنَّعِيمِ
Kana sani a cikin fuskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima.

25 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 025

يُسۡقَوۡنَ مِن رَّحِيقٖ مَّخۡتُومٍ
Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.

26 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 026

خِتَٰمُهُۥ مِسۡكٞۚ وَفِي ذَٰلِكَ فَلۡيَتَنَافَسِ ٱلۡمُتَنَٰفِسُونَ
¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma.

27 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 027

وَمِزَاجُهُۥ مِن تَسۡنِيمٍ
Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.

28 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 028

عَيۡنٗا يَشۡرَبُ بِهَا ٱلۡمُقَرَّبُونَ
(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.

29 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 029

إِنَّ ٱلَّذِينَ أَجۡرَمُواْ كَانُواْ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يَضۡحَكُونَ
Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.

30 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 030

وَإِذَا مَرُّواْ بِهِمۡ يَتَغَامَزُونَ
Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.

31 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 031

وَإِذَا ٱنقَلَبُوٓاْ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِمُ ٱنقَلَبُواْ فَكِهِينَ
Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.

32 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 032

وَإِذَا رَأَوۡهُمۡ قَالُوٓاْ إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ لَضَآلُّونَ
Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne."

33 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 033

وَمَآ أُرۡسِلُواْ عَلَيۡهِمۡ حَٰفِظِينَ
Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.

34 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 034

فَٱلۡيَوۡمَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنَ ٱلۡكُفَّارِ يَضۡحَكُونَ
To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya.

35 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 035

عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ
A kan karagu, suna ta kallo.

36 - Al-Mutaffifin (The Defrauding) - 036

هَلۡ ثُوِّبَ ٱلۡكُفَّارُ مَا كَانُواْ يَفۡعَلُونَ
Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?*
* Amsar tambaya "na'am.".

Scroll to Top