النجم
An-Najm
The Star
1 - An-Najm (The Star) - 001
وَٱلنَّجۡمِ إِذَا هَوَىٰ
Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.
2 - An-Najm (The Star) - 002
مَا ضَلَّ صَاحِبُكُمۡ وَمَا غَوَىٰ
Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.
3 - An-Najm (The Star) - 003
وَمَا يَنطِقُ عَنِ ٱلۡهَوَىٰٓ
Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.
4 - An-Najm (The Star) - 004
إِنۡ هُوَ إِلَّا وَحۡيٞ يُوحَىٰ
(Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.
5 - An-Najm (The Star) - 005
عَلَّمَهُۥ شَدِيدُ ٱلۡقُوَىٰ
(Malã'ika) mai tsananin ƙarfi *ya sanar da shi.
* Wahayin da ke zuwa ga Annabi bãbu ɓata a cikinsa dõmin Jibrilu mai kãwo shi ga Annabi, Malã'ika ne mai ƙarfi ƙwarai, wani Shaiɗãni bã ya iya taron sa dõmin ya musanya wahayin, kuma Annabi ya san shi sõsai, kuma idan ya kãwo wahayin, sai ya sauko kusa ƙwarai da Annabi, sa'an nan shi kuma Annabi ba rikitacce ba ne, yanã cikin hankalinsa.
6 - An-Najm (The Star) - 006
ذُو مِرَّةٖ فَٱسۡتَوَىٰ
Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita.
7 - An-Najm (The Star) - 007
وَهُوَ بِٱلۡأُفُقِ ٱلۡأَعۡلَىٰ
Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi daukaka.
8 - An-Najm (The Star) - 008
ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّىٰ
Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa.
9 - An-Najm (The Star) - 009
فَكَانَ قَابَ قَوۡسَيۡنِ أَوۡ أَدۡنَىٰ
Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa.
10 - An-Najm (The Star) - 010
فَأَوۡحَىٰٓ إِلَىٰ عَبۡدِهِۦ مَآ أَوۡحَىٰ
Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa).
11 - An-Najm (The Star) - 011
مَا كَذَبَ ٱلۡفُؤَادُ مَا رَأَىٰٓ
Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba.
12 - An-Najm (The Star) - 012
أَفَتُمَٰرُونَهُۥ عَلَىٰ مَا يَرَىٰ
Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani?
13 - An-Najm (The Star) - 013
وَلَقَدۡ رَءَاهُ نَزۡلَةً أُخۡرَىٰ
Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa.*
* Lamirin Malã'ika Jibrila ne.
14 - An-Najm (The Star) - 014
عِندَ سِدۡرَةِ ٱلۡمُنتَهَىٰ
A wurin da magaryar tuƙẽwa take.
15 - An-Najm (The Star) - 015
عِندَهَا جَنَّةُ ٱلۡمَأۡوَىٰٓ
A inda taken, nan Aljannar makoma take.
16 - An-Najm (The Star) - 016
إِذۡ يَغۡشَى ٱلسِّدۡرَةَ مَا يَغۡشَىٰ
Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta.
17 - An-Najm (The Star) - 017
مَا زَاغَ ٱلۡبَصَرُ وَمَا طَغَىٰ
Ganinsa* bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.
* Lamirin Malã'ika Jibrila ne.
18 - An-Najm (The Star) - 018
لَقَدۡ رَأَىٰ مِنۡ ءَايَٰتِ رَبِّهِ ٱلۡكُبۡرَىٰٓ
Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma* daga ãyõyin Ubangijinsa.
* Watau dai Alƙur'ani ya zo daga Allah ta hanya mafi aminci har ya sadu da mutãne dõmin su yi aiki da abin da ke cikinsa.
19 - An-Najm (The Star) - 019
أَفَرَءَيۡتُمُ ٱللَّـٰتَ وَٱلۡعُزَّىٰ
Shin, kun ga Lãta da uzza?*
* Watau kun bar Alƙur'ani kun kõma wa surkullen da kuke haɗãwa game da gumãka su Lãta da Uzza da Manãta. Kuna cewa sũ wakĩlan Mala'ikun da kuke bautã wa ne kuma su 'ya'yan Allah mãtã ne. Sunã cetonku daga Allah.
20 - An-Najm (The Star) - 020
وَمَنَوٰةَ ٱلثَّالِثَةَ ٱلۡأُخۡرَىٰٓ
Da (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu?
21 - An-Najm (The Star) - 021
أَلَكُمُ ٱلذَّكَرُ وَلَهُ ٱلۡأُنثَىٰ
Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace?
22 - An-Najm (The Star) - 022
تِلۡكَ إِذٗا قِسۡمَةٞ ضِيزَىٰٓ
Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe.
23 - An-Najm (The Star) - 023
إِنۡ هِيَ إِلَّآ أَسۡمَآءٞ سَمَّيۡتُمُوهَآ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلۡطَٰنٍۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَمَا تَهۡوَى ٱلۡأَنفُسُۖ وَلَقَدۡ جَآءَهُم مِّن رَّبِّهِمُ ٱلۡهُدَىٰٓ
Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar* ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton).
* Watau Alƙur'ani wanda Mala'ika jibrĩla ya zo wa Annabi da shi. Sun bar shi sun kõma wa tatsũniyõyi da gũrace-gũrace.
24 - An-Najm (The Star) - 024
أَمۡ لِلۡإِنسَٰنِ مَا تَمَنَّىٰ
Ko (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri?
25 - An-Najm (The Star) - 025
فَلِلَّهِ ٱلۡأٓخِرَةُ وَٱلۡأُولَىٰ
To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure).
26 - An-Najm (The Star) - 026
۞وَكَم مِّن مَّلَكٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ لَا تُغۡنِي شَفَٰعَتُهُمۡ شَيۡـًٔا إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ أَن يَأۡذَنَ ٱللَّهُ لِمَن يَشَآءُ وَيَرۡضَىٰٓ
Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda.
27 - An-Najm (The Star) - 027
إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ لَيُسَمُّونَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ تَسۡمِيَةَ ٱلۡأُنثَىٰ
Lalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan mace.
28 - An-Najm (The Star) - 028
وَمَا لَهُم بِهِۦ مِنۡ عِلۡمٍۖ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّۖ وَإِنَّ ٱلظَّنَّ لَا يُغۡنِي مِنَ ٱلۡحَقِّ شَيۡـٔٗا
Kuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya.
29 - An-Najm (The Star) - 029
فَأَعۡرِضۡ عَن مَّن تَوَلَّىٰ عَن ذِكۡرِنَا وَلَمۡ يُرِدۡ إِلَّا ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا
Sabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambaton Mu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya).
30 - An-Najm (The Star) - 030
ذَٰلِكَ مَبۡلَغُهُم مِّنَ ٱلۡعِلۡمِۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِمَنِ ٱهۡتَدَىٰ
Wannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyar Sa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya.
31 - An-Najm (The Star) - 031
وَلِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ لِيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ أَسَـٰٓـُٔواْ بِمَا عَمِلُواْ وَيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ أَحۡسَنُواْ بِٱلۡحُسۡنَى
Kuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã na Allah kawai ne, dõmin Yã sãka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya sãka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau.
32 - An-Najm (The Star) - 032
ٱلَّذِينَ يَجۡتَنِبُونَ كَبَـٰٓئِرَ ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡفَوَٰحِشَ إِلَّا ٱللَّمَمَۚ إِنَّ رَبَّكَ وَٰسِعُ ٱلۡمَغۡفِرَةِۚ هُوَ أَعۡلَمُ بِكُمۡ إِذۡ أَنشَأَكُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ وَإِذۡ أَنتُمۡ أَجِنَّةٞ فِي بُطُونِ أُمَّهَٰتِكُمۡۖ فَلَا تُزَكُّوٓاْ أَنفُسَكُمۡۖ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَنِ ٱتَّقَىٰٓ
Waɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake* kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa.
* Wanda yake mutumin kirki, Allah Ya san shi. Kada ku dinga tsarkake kanku da bãkunanku dõmin neman girma, kõ dõmin neman wani abu dabam.
33 - An-Najm (The Star) - 033
أَفَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي تَوَلَّىٰ
Shin, ka ga wannan da ya jũya baya?
34 - An-Najm (The Star) - 034
وَأَعۡطَىٰ قَلِيلٗا وَأَكۡدَىٰٓ
Ya yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa?
35 - An-Najm (The Star) - 035
أَعِندَهُۥ عِلۡمُ ٱلۡغَيۡبِ فَهُوَ يَرَىٰٓ
Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin?
36 - An-Najm (The Star) - 036
أَمۡ لَمۡ يُنَبَّأۡ بِمَا فِي صُحُفِ مُوسَىٰ
Ko kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã?
37 - An-Najm (The Star) - 037
وَإِبۡرَٰهِيمَ ٱلَّذِي وَفَّىٰٓ
Da Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari?
38 - An-Najm (The Star) - 038
أَلَّا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰ
Cẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani.
39 - An-Najm (The Star) - 039
وَأَن لَّيۡسَ لِلۡإِنسَٰنِ إِلَّا مَا سَعَىٰ
Kuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata.
40 - An-Najm (The Star) - 040
وَأَنَّ سَعۡيَهُۥ سَوۡفَ يُرَىٰ
Kuma lalle, aikinsa zã a gan shi.
41 - An-Najm (The Star) - 041
ثُمَّ يُجۡزَىٰهُ ٱلۡجَزَآءَ ٱلۡأَوۡفَىٰ
Sa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni?
42 - An-Najm (The Star) - 042
وَأَنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلۡمُنتَهَىٰ
Kuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take?
43 - An-Najm (The Star) - 043
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَضۡحَكَ وَأَبۡكَىٰ
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka.
44 - An-Najm (The Star) - 044
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَمَاتَ وَأَحۡيَا
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar.
45 - An-Najm (The Star) - 045
وَأَنَّهُۥ خَلَقَ ٱلزَّوۡجَيۡنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰ
Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace.
46 - An-Najm (The Star) - 046
مِن نُّطۡفَةٍ إِذَا تُمۡنَىٰ
Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.
47 - An-Najm (The Star) - 047
وَأَنَّ عَلَيۡهِ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأُخۡرَىٰ
Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take.
48 - An-Najm (The Star) - 048
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَغۡنَىٰ وَأَقۡنَىٰ
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar.
49 - An-Najm (The Star) - 049
وَأَنَّهُۥ هُوَ رَبُّ ٱلشِّعۡرَىٰ
Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira.*
* Sũnan wasu taurãri biyu ne sunã fita a bãyan taurarin Jauza'a sunã tafiya daga kudu zuwa arewa karkace. Kabĩlar Lãrabãwa ta Khuza'a na bauta musu da umurnin Abu Kabshah, ɗaya daga cikin kãkannin Annabi na wajen uwa dõmin haka ne Ƙuraishãwa ke ce wa Annabi Ibn abĩ Kabshah, wanda ya ƙãga sãbon addinĩn da ya sãɓawa na ubanninsa.
50 - An-Najm (The Star) - 050
وَأَنَّهُۥٓ أَهۡلَكَ عَادًا ٱلۡأُولَىٰ
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko.
51 - An-Najm (The Star) - 051
وَثَمُودَاْ فَمَآ أَبۡقَىٰ
Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba.
52 - An-Najm (The Star) - 052
وَقَوۡمَ نُوحٖ مِّن قَبۡلُۖ إِنَّهُمۡ كَانُواْ هُمۡ أَظۡلَمَ وَأَطۡغَىٰ
Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai.
53 - An-Najm (The Star) - 053
وَٱلۡمُؤۡتَفِكَةَ أَهۡوَىٰ
Da waɗanda aka birkice *ƙasarsu, Ya kãyar da su.
* Mutãnen Lũɗu da aka birkice ƙasarsu da su.
54 - An-Najm (The Star) - 054
فَغَشَّىٰهَا مَا غَشَّىٰ
Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su.
55 - An-Najm (The Star) - 055
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكَ تَتَمَارَىٰ
To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake *yin shakka?
* Kamar abõkin magana kõ mai karãtu.
56 - An-Najm (The Star) - 056
هَٰذَا نَذِيرٞ مِّنَ ٱلنُّذُرِ ٱلۡأُولَىٰٓ
wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko.
57 - An-Najm (The Star) - 057
أَزِفَتِ ٱلۡأٓزِفَةُ
Makusanciya* fa, tã yi kusa.
* Makusanciya ita ce Ƙiyãma.
58 - An-Najm (The Star) - 058
لَيۡسَ لَهَا مِن دُونِ ٱللَّهِ كَاشِفَةٌ
Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta.
59 - An-Najm (The Star) - 059
أَفَمِنۡ هَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ تَعۡجَبُونَ
Shin, kuma daga wannan *lãbãri kuke mãmãki?
* Al'ƙur'ãni.
60 - An-Najm (The Star) - 060
وَتَضۡحَكُونَ وَلَا تَبۡكُونَ
Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka?
61 - An-Najm (The Star) - 061
وَأَنتُمۡ سَٰمِدُونَ
Alhãli kunã mãsu wãsã?
62 - An-Najm (The Star) - 062