القارعة
Al-Qari'ah
The Calamity
1 - Al-Qari'ah (The Calamity) - 001
ٱلۡقَارِعَةُ
Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!
2 - Al-Qari'ah (The Calamity) - 002
مَا ٱلۡقَارِعَةُ
Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?
3 - Al-Qari'ah (The Calamity) - 003
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡقَارِعَةُ
Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?
4 - Al-Qari'ah (The Calamity) - 004
يَوۡمَ يَكُونُ ٱلنَّاسُ كَٱلۡفَرَاشِ ٱلۡمَبۡثُوثِ
Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa.
5 - Al-Qari'ah (The Calamity) - 005
وَتَكُونُ ٱلۡجِبَالُ كَٱلۡعِهۡنِ ٱلۡمَنفُوشِ
Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe.
6 - Al-Qari'ah (The Calamity) - 006
فَأَمَّا مَن ثَقُلَتۡ مَوَٰزِينُهُۥ
To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.
7 - Al-Qari'ah (The Calamity) - 007
فَهُوَ فِي عِيشَةٖ رَّاضِيَةٖ
To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.
8 - Al-Qari'ah (The Calamity) - 008
وَأَمَّا مَنۡ خَفَّتۡ مَوَٰزِينُهُۥ
Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi).
9 - Al-Qari'ah (The Calamity) - 009
فَأُمُّهُۥ هَاوِيَةٞ
To, uwarsa Hãwiya ce.
10 - Al-Qari'ah (The Calamity) - 010
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا هِيَهۡ
Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?
11 - Al-Qari'ah (The Calamity) - 011