Abubuwa guda huɗu wanda ya kasance a cikinsa to ya zama munafiki tsantsa, wanda ya kasance a tare da shi akwai wata ɗabi'a daga cikinsu to ya kasance akwai ɗabi'a ta munafunci a tare da shi har sai ya barta: Idan zai yi magana sai ya yi ƙarya, idan an ƙulla yarjejeniya da shi sai ya yi yaudara, idan ya yi alƙawari sai ya saɓa, idan an yi faɗa da shi sai ya yi fajirci
Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Abubuwa huɗu wanda ya kasance a cikinsu to ya kasance munafiki, idan akwai wata ɗabi'a daga cikinsu a tare da shi to ya kasance yana da ɗabi'ar m…

