'Lallai waɗannan sallolin biyu sune mafi nauyin salloli akan munafuki, da kun san abinda ke cikinsu da kun zo musu koda da jan ciki ne akan gwiwowi
Daga Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallar Asuba wata rana sai ya ce: "Shin wane ya zo ne?" suka ce: A'a, ya ce: "Shin wane ya zo ne?" Suka ce: A'a, ya ce: 'Lallai waɗannan sallol…

