Ya Manzon Allah, dukiyoyi sun halaka hanyoyi sun yanke, ka roƙa mana Allah Ya shayar da mu
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya shiga masallaci a ranar Juma'a ta wata ƙofar da ta kasance daura da gidan hukunci, alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana tsaye yana huɗuba, sai ya fuskanci Manzon Allah…

