Wanda ya yi alwala irin wannan alwalar tawa sannan ya yi sallah raka'a biyu bai zantar da ransa a cikinsu ba, to, Allah Zai gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa
Daga Humran bararran bawa na Usman Dan Affan cewa ya ga Usman Dan Affan ya nemi da akawo masa ruwan alwala, sai ya karkato da kwaryar (butar Alwala), sai ya wankesu sau uku, sannan ya shigar da (hannunsa na) dama a ruwan alwalar, sannan ya kuskure baki ya shaƙa ruwa ya…

