Kada mace ta yi tafiya, tafiyar kwana biyu sai da mijinta tare da ita ko muharraminta
Daga Abu sa'id AlKhudr - Allah Ya yarda da shi - ya kasance ya yi yaƙi tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yaƙi goma sha biyu - ya ce: Na ji abubuwa hudu daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai suka ƙayatar dani,…

