Wannan kalmar ta gaske aljani ya fauceta ne, sai ya yi kyarkyararta a kunnen abokin harkarsa irin kyarkyarar kaza, sai su cakuɗata da ƙarya sama da ɗari
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Wasu mutane sun tambayi Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da bokaye, sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Su ba komai ba ne". Suka ce: Ya Ma’aikin Allah; Wani lokacin suna ba da labari sai kuma abin ya zama gaske. Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; Wannan kalmar ta gaske aljani ya fauceta ne, sai ya yi kyarkyararta a kunnen abokin harkarsa irin kyarkyarar kaza, sai su cakuɗata da ƙarya sama da ɗari.
Explanation
Sai suka ce: Maganarsu tana daidai da abin da ya faru a wani lokaci, kamar a ce su ba da labarin wani abu na gaibu zai faru a wata kaza a rana kaza, sai kuma ya faru kamar yadda suka faɗa.
Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Aljanu suna sato abin da suke ji ne na labarun sama, sai su sauko da shi zuwa ga abokan hulɗarsu cikin bokaye, sai su ba su labarin abin da suka ji, sannan sai shi bokan ya ƙara ƙarya ɗari a kan wannan labarin da ya ji daga sama.
Benefits
An tsare sama daga shaiɗanu da aiko Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da su ji wani abu na wahayi ko waninsa, sai dai wanda ya saci magana ya kuma tsira daga tauraron [harbosu].
Aljanu suna da abokan hulɗarsu cikin mutane
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

