Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wanka, ko ya kasance yana wanka, da sa'i zuwa mudu biyar, kuma yana alwala da mudu
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wanka, ko ya kasance yana wanka, da sa'i zuwa mudu biyar, kuma yana alwala da mudu.
Explanation
Benefits
An so ƙaranta ruwan alwala da wanka gwargwadan buƙata, kuma wannan shi ne shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Abin nufi cikawa a alwala da wanka tare da kula da sunnoni da ladubba ba tare da ɓarna ko ƙwauro ba, kuma a kiyaye lokaci da yawan ruwan da ƙarancinsa da wanin hakan.
Ana anbaton janaba ga dukkan wanda ya zubar da maniyyi ko ya yi jima'i, kuma an anbaceta da hakan dan mai ita yana nisantar sallah da ibadu har sai ya tsarkaka daga gareta.
Sa'i: wani abin awo ne sananne, abin nufi da shi sa'in Annabi, awonsa yakai nauyi (480) na alkama mai kyau, a lita kuma (lita 3).
Mudu: Awone na shari'a, shi cikin tafuka biyu ne na mutum madaidaici idan ya cikasu ya miƙe hannunsa da su. Mudu shi ne ɗaya bisa huɗu na sa'i da haɗuwar masana fiƙihu, gwargwadansa ML (750).
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

