Allah Zai tara mutane na farko da na ƙarshe a bigire ɗaya, mai kira zai jiyar da su kuma gani zai ƙetare su, rana zata kusanto, sai baƙin ciki da takaici ya kai ga mutane abinda ba za su iya ɗauka ba, kuma ba za su iya jurewa ba
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Hurairah - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - an zo masa da wani nama sai aka ɗaga masa zira'i, ya kasance yana ƙayatar da shi sai ya gutsira daga gare shi gutsira (ɗaya), sannan ya ce: "Ni ne shugaban mutane a ranar alƙiyama, shin kun san daga menene hakan? Allah Zai tara mutane na farko da na ƙarshe a bigire ɗaya, mai kira zai jiyar da su kuma gani zai ƙetare su, rana zata kusanto, sai baƙin ciki da takaici ya kai ga mutane abinda ba za su iya ɗauka ba, kuma ba za su iya jurewa ba, sai mutane su ce: Shin bakwa ganin abinda haƙiƙa ya kai muku ? shin bakwa duba wanda zai yi muku ceto zuwa ga Ubangijinku ba? sai wasu daga mutane su ce wa wasu: Ku je gurin (annabi) Adam, sai su zo wa Adam - aminci ya tabbata agare shi - sai su ce masa: Kai ne uban mutane, Allah Ya halicceka da hannunSa, kuma Ya busa maka daga ranSa, kuma Ya umarci mala'iku sai suka yi maka sujjada, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa, shin baka gani zuwa abinda ya kai mana? sai Adam ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushi a yau bai taba irin wannan fushin ba, kuma ba zai taba yin irin wannan fushin ba, kuma lallai ni hakika Ya hanani daga bishiya sai na saba maSa, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Nuhu.
Sai su zo wa (annabi) Nuhu sai su ce: kai Nuhu, lallai kai ne farkon manzanni zuwa mutanen kasa, hakika Allah Ya ambaceka bawa mai yawan godiya, shin baka ganin abinda muke cikinsa, shin baka gani zuwa abinda ya kai mana, shin baka nema mana ceto ga Ubangijinka ba? sai ya ce: Lallai Ubangijina Ya yi fushi a yau bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa ba, kuma lallai cewa ni akwai mummunar addu'ar da na yi akan mutanena, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi gurin (annabi) Ibrahim.
Sai su zo wa (annabi) Ibrahim sai su ce: kai Ibrahim, kai ne Annabin Allah kuma badaɗayinSa daga mutanen ƙasa, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai ya ce musu: Lallai Ubangijina haƙiƙa Ya yi fushi a yau fushin da bai taɓa fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa ba irinsa, lallai cewa ni na yi ƙarya sau uku, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa ga (annabi) Musa.
Sai su zo wa (annabi) Musa sai su ce: Kai Musa kaine Manzon Allah, Allah Ya fifitaka da saƙonninSa da kuma zancenSa akan mutane, ka nema mana ceto ga Ubangijnka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushin da bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, lallai ni naa kashe wani rai da ba'a yi umarni da in kasheta ba, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Isa.
Sai su zo wa (annabi) Isa sai su ce: kai Isa, kaine Manzon Allah kuma kalmarSa da ya jefata zuwa Maryam kuma rai daga gareShi, kuma ka yi wa mutane magana a cikin shinfidar goyo, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai Isa ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushin da bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, ba zai anbaci wani zunubi ba, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -".
Sai su zo wa (annabi) Muhammad sai su ce kai ne Manzon Allah kuma cika makin Annabawa, hakika Allah Ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubinka da abinda ya jinkirta, ka nema mana ceto zuwa ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai in tafi, sai in zo ƙarƙashin al’arshi sai infaɗi ina mai sujjada ga Ubangina, sannan Allah Ya buɗe mini daga godiyarSa da kyakkyawan yabo gareShi na wani abinda bai taɓa buɗewa wani a gabani na ba, sannan a ce: Ya Muhammad ka ɗago kanka, ka yi tambaya za'a baka shi, ka nemi ceto za'a baka ceto, sai in dago kaina, sai in ce: Al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Uabngiji, sai ace: Ya Muhammad ka shigar daga al'ummarka wadanda babu wani hisabi akansu ta kofar dama daga kofofin aljanna, kuma su suna tarayya da mutane a koma bayan haka na kofofi".
sannan ya ce: "Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, lalai tsakanin ginshikai biyu daga ginshikan aljanna kamar tsakanin Makka ne da Hajar, ko tsakanin Makka ne da Busra".
Explanation
Benefits
Fifita Annabinmu - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan dukkan mutane.
AlƘali Iyad ya ce; An ce: Shugaba wanda ya wuce mutanensa kuma ake komawa zuwa gare shi acikin tsanani, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne shugabansu a duniya da lahira, kaɗai Ya keɓanci ranar alƙiyama ne dan ɗaukakar shugabanci a cikinta, da kuma miƙa wuyan gabaɗayansu gare shi, kuma saboda kasancewar (annabi) Adam da dukkan 'ya'yansa ƙarƙashin tutarsa ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Hikima a cikin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi musu ilhamar tambayar (annabi) Adam, da waɗanda ke bayansa a farko, ba'ayi musu ilhamar tambayar Annabinmu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba, dan bayyanar da falalarsa, shi ne ƙarshe a ɗaukakar matsayi, da kuma cikar kusanci.
An shara'anta ga wanda yake son wata buƙata daga bawa ya gabatar da siffar abin tambaya da mafi kyan siffofinsa a gabansa; dan ya zama mafi kira ga amsawa.
Yana halatta ga wanda aka tambaya daga wani al'amarin da ba shi da iko a kansa ya yi hanzari da abinda za'a karɓa daga gare shi, an so a nunar ga wanda ake zatan cewa shi ne mafi iko akan hakan.
Bayanin tsoron tsayuwa (alƙiyama) da tsananin taron akan bayi a ranar alƙiyama.
Tawadu'in Annabi, inda suka ambaci abinda ya wuce daga gare su; dan cewa su koma bayan wannan matsayar ne.
Tabbatar da ceto mafi girma a ranar alƙiyama, hakan dan rabewa ne tsakanin halittu.
Tabbaatar da Wasila da matsayi abin yabo ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Godiya ga Allah - Maɗaukkain sarki - da yabo basa ƙarewa, saboda haka ne Allah Zai buɗewa ManzonSa a wannan matsayar na kyakkyawan yabo gare shi abinda bai taɓa buɗe shi ga wani kafinsa ba.
Bayanin cewa al'ummar (annabi) Muhammad ita ce mafificiyar al'ummu, to su suna da wasu keɓantattun abubuwa a cikin shiga aljanna, inda waɗanda basu da wani hisabi akansu zasu shiga daga wata keɓantacciyar ƙofa garesu, kuma zasu yi tarayya da mutane a ragowar ƙofofin.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

