Mai wuce wa ta gaban mai sallah da ya san abin da ke kan shi na zunubi, to ya tsaya arba'in shi ne mafi alheri gareshi da ya wuce ta gabansa
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Busr Ibnu Sa'id cewa Zaid Ibnu Khalid al-Juhani - Allah Ya yarda da shi -, ya aike shi zuwa wajen Abu Juhaim - Allah Ya yarda da shi -, yana tambayarsa me ya ji daga wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a sha'anin wanda ya wuce ta gaban mai yin sallah? Abu Juhaim ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Mai wuce wa ta gaban mai sallah da ya san abin da ke kan shi na zunubi, to ya tsaya arba'in shi ne mafi alheri gareshi da ya wuce ta gabansa» Abu-al-Nadhr ya ce: Ban sani ba shin ya ce: Kwanaki arba'in ya ce ko wata ko shekara?
Explanation
Benefits
Ibnu Hajar ya ce: An yi saɓani a iyankance haka, an ce idan ya wuce tsakaninsa da tsakanin gwargwadan sujjadarsa, kuma an ce tsakaninsa da tsakaninsa gwargwadan zira'i uku, kuma an ce tsakaninsa da stakaninsa gwargwadan jifan dutse.
Suyuɗi ya ce: Abin nufi da wucewa ta gabansa yana mai bijirewa, amma da a ce idan ya yi tafiya ta gabansa yana mai tafiya ta fuskar alƙibla to bai zama mai shiga cikin narkon ba.
Abinda ya fi ga mai yin sallah shi ne kada ya yi sallah a hanyoyin mutane, da kuma guraren da babu makawa sai sun wuce ta gurin, dan kada ya bijirar da sallarsa ga tawaya, kuma a bijro wa mai wucewar ga zunubi, kuma wajibi ne a kansa ya sami sutra da kariya tsakaninsa da tsakanin mai wucewar.
Ana fahimta daga gare shi cewa zunubin da ya jerantu akan saɓo a lahira ko da ya ƙaranta to mai girma ne daga kowace wahla a duniya duk yanda ta tsananta.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

