Duk abin da na haneku daga gare shi to ku nisance shi, kuma abinda na umarce ku da shi to ku zo da shi dai dai iyawarku
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: «Duk abin da na haneku daga gare shi to ku nisance shi, kuma abinda na umarce ku da shi to ku zo da shi dai dai iyawarku, domin abin da ya halaka magabatanku (shi ne) yawan tambayoyinsu da kuma saɓawarsu ga Annabawansu».
Explanation
Benefits
Hani, ba’a yi rangwami akan aikata wani abu daga gare shi ba, umarni kuma an ƙayyade shi da gwargwadan iko; domin bari abin ƙaddarawa ne, aiki kuma yana buƙatuwa zuwa ga iko akan samar da aikin da aka yi umarni da shi.
Hani akan yawan tambaya, haƙiƙa malamai sun raba tambaya gida biyu: Ta ɗayansu: Wadda take kasancewa ta fuskar koyarwa ga abinda ake buƙatuwa zuwa gare shi na al'amarin addini, to wannan an yi umarni da ita, daga wannan nau'in tambayoyin sahabbai suke. Na biyu: Wadda ta kasance ta fuskar ta'annuti da ɗorawa kai to wannan ita ce wacce aka hana.
Gargaɗin wannan al'ummar daga saɓawa annabinta, kamar yadda ya afku a cikin al’ummun da suka gabata.
Abin da aka hana yana ƙunsar kaɗan da mai yawa; domin nisantarsa ba ya yi wu wa sai da nisantar ƙanƙaninsa da mai yawansa, misali: Ya hanemu daga riba to hanin ya ƙunshi ƙanƙaninta da kuma mai yawanta.
Barin sabubban da zasu iya kaiwa zuwa ga haram; domin hakan yana daga ma'anar nisanta.
Ba ya kamata ga mutum idan ya ji umarnin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce ba: Shin wajibi ne ko mustahabbi ne, kawai ya wajaba a kansa ya yi gaggawa zuwa aikata shi; saboda faɗinsa: «Ku zo da shi gwargwadan iyawarku».
Yawan tambayoyi sababi ne na halaka musamman ma a cikin al'amuran da ba zai yi wu akai zuwa garesu ba, misali mas'alolin gaibu, da siffar yanayin ranar alƙiyama, kada ka yawaita tambaya a cikinsu sai ka halaka, sai ka zama mai tsanantawa a cikin Addini mai zirfafawa.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

