Duk wanda ya farar da wani abu a cikin wannan Addinin namu wanda ba ya ciki, to shi abun mayarwa ne
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga uwar muminai Babar Abdullahi Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -, ta ce: Manzon Allah - tsira amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Duk wanda ya farar da wani abu a cikin wannan Addinin namu wanda ba ya ciki, to shi abun mayarwa ne». A cikin wata riwaya ta Muslim: «Wanda ya aikata wani aikin da babu umarninmu a cikinsa to shi abin mayarwa ne».
Explanation
Benefits
Addini ba ra'ayi ba ne, ko ganin kyan abu, kadai da bin Manzon Allah ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Wannan hadisin dalili ne akan cikar Addini.
Bidi'a ita ce dukkanin abinda aka farar a Addini wanda babu shi a lokacin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, da sahabbansa na akida ne ko magana ko aiki.
Wannan Hadisin tushe ne daga tushen Musulunci, shi kamar ma'auni ne ga ayyuka, kamar yadda kowanne aikin da ba'a nufi zatin Allah - madaukakin sarki - da shi ba, to mai aikata shi ba shi da wani lada, hakanan kowanne aikin da bai zama ya dace da abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo da shi ba to shi abin juyarwa ne akan mai aikata shi.
Hadisin wata ƙa'idace a kan mayar da bidi'io'in da aka ƙirƙira da kuma abubuwa munkarai masu afkuwa.
Fararrun abubuwan da aka hana su ne abinda suka kasance na al'amuran Addini, ba na duniya ba.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

