Lallai za'a samu wasu fitintinu, ku saurara sannan a samu wasu fitintinu wanda ke zaune a cikinsu ya fi wanda ke tafiya a cikinsu, mai tafiya ya fi wanda ke gaggawa zuwa garesu,
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Usman al-Shahhaam, ya ce: Ni da Farƙad al-Sabakhi mun tafi zuwa wurin Muslim ɗan Abu Bakrata alhali yana ƙasarsa, sai muka je wurinsa sai muka ce: Shin ka ji babanka yana zantarwa da wani hadisi a game da fitintinu? ya ce: Eh, na ji Abu Bakrata - Allah Ya yarda da shi - yana zantarwa, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai za'a samu wasu fitintinu, ku saurara sannan a samu wasu fitintinu wanda ke zaune a cikinsu ya fi wanda ke tafiya a cikinsu, mai tafiya ya fi wanda ke gaggawa zuwa garesu, ku saurara idan suka sauka ko suka faru wanda yake da raƙuma to ya riski raƙumansa, wanda yake da tumakai to ya riski tumakansa, wanda yake da wata ƙasa to ya risku da ƙasarsa», ya ce sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah to kana ganin wanda ba shi da raƙuma ko tumakai ko ƙasa fa? ya ce: «Ɗayanku ya nufi takobinsa sai ya caka tsinin takobin a dutse, sannan ya tsira idan zai iya tsira, ya Allah shin na isar? ya Allah shin na isar?». Ya ce: sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah shin kana ganin idan aka tilastani har aka tafi da ni zuwa daya daga jama'a biyun, ko daya daga bangarori biyun, sai wani mutum ya dakeni da takobinsa, ko wata kibiya ta zo sai ta kasheni? ya ce: "Zai koma da zunubinsa da kuma zunubinka, kuma ya zama daga 'yan wuta".
Explanation
Benefits
Nawawi ya ce; Faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (Wanda ke a zaune ya fi wanda ke tsaye), har zuwa ƙarshensa, to ma'anarsa bayanin girman haɗarinsu, da kwaɗaitarwa akan nisantarsu, da guje musu, kuma cewa sharrinsu da fitinarsu zai zama akan gwargwadan rataya da su.
Nawawi ya ce: An ɗauke zunubi ga wanda aka tilastawa akan halartar wurin, amma kisa ba'a halatta shi da tilastawa, kai wanda ya tilasta ɗin zai yi laifi akan wanda aka umarta da shi da ijma'in malamai.
Ibnu Hajar ya ce: Wasu sun ce ; Idan wata ƙungiya ta yi wa shugaba tawaye sai ta hanu daga wajibin da ke kanta ta kuma kafa yaƙi to ya wajaba a yaƙeta, haka nan da ƙungiyoyi biyu zasu yi yaƙi to ya wajaba akan kowane mai iko ya riƙe hannun mai kuskuren da kuma taimakon wanda ke kan gaskiya, wannan ita ce maganar jumhur, wasu kuma suka rarrabe bayani, sai suka ce; Dukkan yaƙin da ya faru tsakanin ƙungiyoyi biyu daga musulmai inda babu wani shugaba ga jama'a to yaƙi a lokacin an hana, sai a saukar da hadisan da ke cikin wannan babin da waninsa akan haka.
Nawawi ya ce: Haƙiƙa malamai sun yi saɓani a yaƙi lokacin fitina, sai wasu suka ce: Ba zai yi yaƙi ba a lokacin fitintinu tsakanin musulmai koda sun shiga gidansa, kuma sun nemi kashe shi, to ba ya halatta ya kare kansa; domin mai neman mai tawili ne, wannan ita ce mazahabar Abu Bakrata sahabi - Allah Ya yarda da shi - da waninsa, Ibnu Umar da Imran ɗan Hussain - Allah Ya yarda da su - da wasunsu suka ce: Ba zai shiga cikinta ba, sai dai idan ya yi nufin kare kansa, to waɗannan mazahabobi biyun sun haɗu akan barin shiga a dukkanin fitintinun Musulunci, mafi yawancin sahabbai da tabi'ai da gamewar maluman Musulunci suka ce: Ya wajaba a taimaki mai gaskiya a lokacin fitintinu, da tsayuwa tare da shi dan kashe 'yan tawaye kamar yadda Madaukakin sarki Ya ce: {To ku kashe wacce ta yi zalincin har sai ta koma zuwa umarnin Allah...} karanta ayar har karshenta, wannan shi ne ingantacce, kuma sun fassara hadisan akan wanda gaskiya ba ta bayyana gare shi ba, ko akan kungiyoyi biyun masu zalinci babu tawili ga wata daga cikinsu.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

