Babu wani musulmin da wata musiba zata same shi, sai ya faɗi abinda Allah Ya umarce shi: {Lallai mu daga Allah muke kuma lallai cewa mu zuwa ga Allah zamu koma} [al-Baƙara: 156], ya Allah Ka bani lada a cikin wannan musibar tawa kuma Ka musanya mini da mafi alheri da ita, sai Allah Ya musanya masa da mafi alheri daga ita
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Ummu Salamah Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Babu wani musulmin da wata musiba zata same shi, sai ya faɗi abinda Allah Ya umarce shi: {Lallai mu daga Allah muke kuma lallai cewa mu zuwa ga Allah zamu koma} [al-Baƙara: 156], ya Allah Ka bani lada a cikin wannan musibar tawa kuma Ka musanya mini da mafi alheri da ita, sai Allah Ya musanya masa da mafi alheri daga ita", ta ce: Lokacin da Abu Salama ya rasu na ce: Waye a cikin musulmai ya fi Abu Salama alheri? farkon gidan da ya yi hijra zuwa ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan sai na faɗeta (addu'ar), sai Allah Ya maye mini gurbinsa da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Explanation
Benefits
Fuskantar da addu'a zuwa ga Allah a cikin musibu da suke sauka; domin canji yana gare shi (shi Allah).
Larurar mumini ya yi ruko da umarnin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - koda hikima bata bayyana daga umarninsa ba.
Alheri dukkansa yana cikin ruko da umarnin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

