HadeethEnc · 1.25.0
Wanda ya bar Juma'o'i uku dan wulaƙantar da su Allah zai yi yumƙi akan zuciyarsa
Available translations
Choose an available translation of this Hadeeth
01
Hadeeth text
Daga Abul Ja'ad al-Damri - Allah Ya yarda da shi -, kuma ya kasance sahabi ne, cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya bar Juma'o'i uku dan wulaƙantar da su Allah zai yi yumƙi akan zuciyarsa".
02
Explanation
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga barin sallar Juma'a, kuma wanda ya bar sallar Juma'a sau uku dan sakaci da kasawa ba tare da wani uzuri ba Allah zai rufe zuciyarsa ta hanyar hana isar alheri gare shi .
03
Benefits
Ibnul Munzir ya hakaito Ijma'i akan cewa sallar Juma'a farilla ce ta aini (wato ta hau kan kowa).
Narko akan wanda ya bar Juma'a dan sakaci shi ne Allah zai yi yumƙi akan zuciyarsa.
Wanda ya bar Juma'a dan wani uzuri to shi ba ya shiga cikin narkon.
Al-Shaukani ya ce: Faɗinsa: (Juma'o'i uku), yana ɗaukar cewa ana nufin faruwar barin kai tsaye daidai ne Juma'o'in a jere ne ko sun rarrabu, hatta da a ce duk shekara zai bar Juma'a ɗaya da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi yumƙi akan zuciyarsa bayan ta uku shi ne zahirin hadisin, kuma zai iya ɗaukar cewa ana nufin Juma'o'i ukun a jere.

Attribution
[Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi]
Categories
Share
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares