Da a ce mutane suna sanin abinda ke cikin kiran sallah (na lada) da kuma sahu na farko sannan ba za su samu ba sai idan sun yi ƙuri'a a kansa da sun yi ƙuri'a
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Da a ce mutane suna sanin abinda ke cikin kiran sallah (na lada) da kuma sahu na farko sannan ba za su samu ba sai idan sun yi ƙuri'a a kansa da sun yi ƙuri'a, kuma da a ce suna sanin abinda ke cikin gaggawa (zuwa sallah a farkon lokaci) da sun yi gasar zuwa gare shi, kuma da a ce suna sanin abinda ke cikin sallar dare (Issha) da Asuba da sun zo musu koda da jan ciki ne».
Explanation
Benefits
Bayanin falalar sahun farko, da kuma kusanci ga liman.
Bayanin falalar gaggawa zuwa sallah a farkon lokacinta da akafi so; dan abinda ke cikinsa na falala mai girma, da kuma abinda ke biye da shi na fa'idoji, daga cikinsu akwai: Riskar sahun farko, da riskar sallah a farkon lokacinta, da yin nafila, da karatun AlƘur'ani, da samun istigfarin mala'iku gare shi, kuma cewa shi ba zai gushe ba acikin sallah muddin dai ya jiran sallah, da wanin hakan.
Kwaɗaitarwa mai girma akan halartar jam’i na waɗannan sallolin biyu, da falala mai yawa a cikin hakan dan abinda ke cikinsu na wahala akan rai na gurɓata farkon baccinta da kuma ƙarshensa, saboda haka ne suka zama mafi nauyin sallah akan munafukai.
Nawawi ya ce: A cikinsa akwai tabbatar da ƙuri'a a cikin haƙƙoƙin da mutane suke cunkoso a kansu kuma suke jayya a cikinsu.
Sahun farko ya fi na uku, na uku yafi na huɗu, da dai sauransu.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

