Lallai bawa zai yi sallah, ba za'a rubuta masa wani abu daga gareta ba sai ushurinta (daya cikin goma), sai ɗaya bisa taranta, sai ɗaya bisa bakwanta, sai ɗaya bisa shidanta, sai ɗaya bisa biyar ɗinta, sai ɗaya bisa huɗunta, sai ɗaya bisa ukunta, sai rabinta
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abdullahi Ibnu Anamah, ya ce: Na ga Ammaru Ibnu Yasir ya shiga masallaci sai ya yi sallah, sai ya sauƙaƙa sallar (wato bai dadeba), ya ce: Lokacin da ya fita, sai na tashi zuwa gare shi, sai na ce: Ya Aba Yaƙazan, haƙiƙa ka sauƙaƙa, ya ce: Shin ka ga na rage wani abu daga ka’idojinta?! Na ce: A'a, ya ce: Lallai ni na gaggautata ne dan gudun waswasin shaiɗan, na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: «Lallai bawa zai yi sallah, ba za'a rubuta masa wani abu daga gareta ba sai ushurinta (daya cikin goma), sai ɗaya bisa taranta, sai ɗaya bisa bakwanta, sai ɗaya bisa shidanta, sai ɗaya bisa biyar ɗinta, sai ɗaya bisa huɗunta, sai ɗaya bisa ukunta, sai rabinta».
Explanation
Benefits
Neman tabbatarwa da kuma tambaya kafin yin inkari.
wadatuwa a bada amsa game da tambaya da kuma rikitarwa, da faɗin maganar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Tawayar ladan sallah da tawayar khushu'i da tadabburin ma'anoninta a cikinsa.
Kwaɗaitarwa mai ƙarfi da kuma zaburarwa mai tsanani akan yin khushu'i a cikin sallah da kuma halarto da zuciya tare da Allah - Maɗaukakin sarki -.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

