Wanda ya sallaci irin sallarmu kuma ya fuskanci alƙiblarmu, kuma ya ci yankanmu to wannan shine muslmin da yake da alƙawarin Allah da alƙawarin ManzonSa, dan haka kada ku warware alƙawarin Allah
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Wanda ya sallaci irin sallarmu kuma ya fuskanci alƙiblarmu, kuma ya ci yankanmu to wannan shine muslmin da yake da alƙawarin Allah da alƙawarin ManzonSa, dan haka kada ku warware alƙawarin Allah».
Explanation
Benefits
Al'amarin mutane abin ɗauka ne akan zahiri banda baɗini, wanda ya bayyanar da alamomin addini za'a gudanar da hukunce-hukuncen Musulmai a kansa muddin dai bai gudanar da saɓanin hakan ba.
Ibnu Rajab ya ce: Ambatan fuskantar alƙibla nuni ne zuwa cewa babu makawa da zuwa da sallar musulmai wacce aka shara'anta a cikin littafinsu wanda aka saukar ga annabinsu ita ce sallah da fuskantar Ka'aba, inba haka bafa wanda ya yi sallah zuwa Baitul Maƙdisi bayan anshafeta kamar Yahudawa ko kallan gabas kamar Nasara to ba musulmi ba ne, koda ya yi shaidar tauhidi.
A cikinsa akwai dalili akan girman gurin fuskantar alƙibla a sallah, domin cewa a cikin sharuɗɗan sallah bai ambaci waninta ba, kamar tsarki da waninsa.
Ibnu Rajab ya ce: Amabatansa cin yankan musulmai a cikinsa akwai nuni zuwa cewa babu makawa daga lazimtar dukkanin shari'un musulunci na zahiri, kuma mafi girmansu shine cin yankan musulmai, da kuma dacewa da su a cikin yankansu, duk wanda ya hanu daga hakan to ba musulmi ba ne.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

