Wata aya a cikin littafinku kuna karantata, da a ce agurinmu mu Yahudawa ta sauka da mun riƙi ranar idi
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Umar Ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum daga cikin Yahudawa ya ce masa: Yakai sarkin muminai, Wata aya a cikin littafinku kuna karantata, da a ce agurinmu mu Yahudawa ta sauka da mun riƙi ranar idi, ya ce: Wacce aya ce? ya ce: {A yau ne na cika muku Addininku kuma na cika muku ni'imata kuma na yardar muku da Musulunci a matsayin Addini} [al-Ma'ida: 3] Umar ya ce: Haƙiƙa mun san wannan ranar, da gurin da ta sauka ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikinsa alhali shi yana tsaye a Arfa a ranar Juma'a.
Explanation
Benefits
Wannan ayar a cikinta akwai bayanin abin da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi baiwa da shi ga wannan al'ummar, inda Ya cika mata Addininta, kuma Ya cika mata ni'imominSa, yadda bata buƙatar wani ƙari a cikin al'amarin Addini, duk abin da ya faru bayan Allah - Maɗaukakin sarki - Ya cika shi, in da ba shi da wani dalili daga gare shi da ake la'akari da shi (a matsayin) bidi'a ɓatacciya, kamar yadda hakan ya tabbata daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Duk wanda ya farar (da wani abu) a cikin al'amarinmu wannan abin da ba ya daga cikinsa, to shi abin juyarwa ne".
Wannan hadisin za'a iya fahima daga gare shi cewa bukukuwan Idi basa kasancewa da ra'ayi da kuma ƙirƙira kamar yadda wasu daga cikin mazowa Littafi (Yahudawa da Nasara) daga gabaninmu suke aikata shi; kawai yana kasancewa ne da shari'a da kuma bi, to wannan ayar yayin da ta ƙunshi cika Addini da cika ni'imar da Allah Ya saukar da ita a cikin ranar da ya shara'antata idi ga wannan al'ummar ta fuska biyu: Na farkonsu: Cewa ita ce ranar idin mako ita ce ranar Juma'a. Na biyu: Ita ce ranar idin babbaban taro , ita ce lokacin taruwarsu mafi girma kuma wurin tsayuwarsu mafi girma (wato Arafat, ga Musulmai).
Sa'adi ya faɗa a cikin tafsirin wannan ayar: {A yau ne Na cika muku Addininku} ta hanyar cikar nasara, da cika shari'u na zahiri da baɗini, tushe da kuma rassa, saboda haka ne Alkur’ani da Hadisi suka kasance sun isa dukkanin isa a cikin hukunce-hukuncen Addini, tushensa da kuma rassansa, duk mai ɗorawa kansa aiki wanda yake riya cewa babu makawa ga mutane a cikin sanin aƙidunsu da kuma hukunce-hukuncensu zuwa wasu ilimai waɗanda ba ilimin Littafi da sunnah ba, na ilmul kalam da waninsa, to shi jahili ne, mai ɓarna a cikin da'awarsa, ya riya cewa Addini ba ya cika sai da abin da ya faɗe shi kuma ya yi kira zuwa gare shi, wannan yana daga cikin mafi girman zalinci da dangantawa Allah da ManzonSa jahilci, {Kuma Na cika muku ni'imata} ta zahiri da baɗini {Kuma na yardar muku da Musulunci a matsayin Addini} wato: Na zaɓar muku shi a matsayin Addini, kamar yadda na yardar muku da shi, sai ku tsaya a kansa dan godiya ga Ubangijinku, ku gode maSa abin da Ya yi muku baiwa da mafificin Addinai kuma mafi ɗaukakarsu kuma mafi cikarsu.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

