a'a ku ce: Mun ji mun bi, muna neman gafarKa ya Ubangijinmu makoma tana wurinKa
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Lokacin da (ayar): {Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa na Allah ne, idan kun bayyanar da abin da ke cikin ranku ko kuka ɓoyeshi Allah zai yi muku hisabi da shi, Yana gafartawa wanda Ya so kuma Yana azabtar da wanda Ya so, Allah Mai iko ne akan dukkan komai}.
[al-Baƙara: 284] ta sauka, ya ce: Sai hakan ya tsananta ga sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - , sai suka zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sannan suka durƙusa akan gwiwowinsu, sai suka ce: Ya Manzon Allah, an ɗora mana ayyukan da zamu iya, sallah da azimi da jihadi da sadaka, haƙiƙa an saukar maka wannan ayar kuma ba zamu iyata ba, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Shin kuna son ku faɗi kamar yadda mazowa littafi biyu a gabaninku suka faɗa, mun ji mun saɓa?a'a ku ce: Mun ji mun bi, muna neman gafarKa ya Ubangijinmu makoma tana wurinKa», suka ce: Mun ji kuma mun bi ya Ubangijinmu gafararKa muke nema makoma tana wurinKa, lokacin da mutane suka karantata, sai harsunansu suka horu da ita, a bayanta sai Allah Ya saukar da {Manzo ya yi imani da abin da aka saukar masa daga Ubangijinsa haka ma muminai, kowannensu ya yi imani da Allah da mala'ikunSa da littattafanSa da ManzanninSa bama banbanta wani daga cikin ManzanninSa, suka ce: Mun ji mun bi ya Ubangijinmu gafararKa muke nema makoma tana wurinKa}.
[al-Baƙara: 285], lokacin da suka aikata hakan sai Allah Ya shafe ta, sai ya saukar da {Allah ba Ya ɗorawa wata rai sai abin da zata iya, abin da ta aikata nata ne, haka abin da ta aikata na laifi yana kanta, ya Ubangijinmu kada Ka kamamu idan muka yi kuskure ko muka manta} [al-Baƙara: 286], ya ce: «Eh» {Ya Ubangijnmu kada Ka ɗora mana wani nauyi kamar yadda ka ɗorawa waɗanda ke gabanmu} [al-Baƙara: 286], ya ce: «Eh», {Ya Ubangijinmu kada ka ɗora mana abin da bazamu iya ba} [al-Baƙara: 286], ya ce: «Eh», {Ka yi mana rangwami Ka gafarta mana Kajiƙanmu Ka taimakemu akan mutane kafirai} [al-Baƙara: 286].
Explanation
Benefits
Tabbatar da share hukunci a cikin Alƙur'ani mai girma, kuma hakan daga cikin Alƙur'ani akwai abin da ake karantawa sai dai an shafe hukuncinsa ba'a yin aiki da shi.
Falalar sahabbai - Allh Ya yarda da su - da ƙaƙandar da kansu, da miƙa lamarinsu ga Allah, da kumq rukonsu da umarnin ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake a kansa na tsananin tsoronSa ga al'ummarsa kada ta shiga inda al'ummun da suka wuce suka shiga na kin karbar abin da aka zo musu da shi na umarce-umarcen Allah - Maɗaukakin sarki -.
Wajabcin miƙa wuya ga umarnin Allah - Maɗaukakin sarki -, da kiyayewa daga bijirewa umarninsa, kuma cewa wannan a cikinsa akwai kamanceceniya ga mazowa littafi (Yahudu da Nasara).
Bayanin falalar wannan al'ummar akan al'ummun da suka gabata, inda suka cewa Annbawansu: Mun ji kuma mun saɓa, wannan al'ummar kuma ta ce: Mun ji kuma mun bi.
Falalar wannan al’ummar a ɗauke mata ƙunci da kuma amsa addu'a da kuma rashin kamata da mantuwa da kuma kuskure, da ɗauke nauyace-nauyacen dake kan waɗanda ke gabaninsu daga gareta, da kuma rashin ɗora mata abin da ba zata iya ba.
Allah - tsarki ya tabbatar maSa - ba Ya ɗora mana abin da ba zamu iya shi ba, kuma ba Ya ɗora mana wani abu sai abin da zamu iya, kuma cewa wasiwasin da suke yawo a cikin ƙirazanmu idan bamu karkata garesu ba, kuma bamu natsu a garesu ba, kuma ba mu yi riƙo dasu ba to basa cutarwa.
Wannan addu'ar Allah - Maɗaukakin sarki - Ya bada labarinta ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da kuma muminai, kuma Ya sanyata a cikin littafinSa; dan ta zama addu'ar wanda zai zo bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da sahabbai - Allah Ya yarda da su -, ita tana daga cikin addu'ar da yake kamata a haddaceta, kuma a yi addu'a da ita (a lokuta) da yawa.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

