Ya ɗanɗani ɗanɗanon imani wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammadu a matsayin Manzo
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abbas ɗan Abdulmuɗɗalib - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Ya ɗanɗani ɗanɗanon imani wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammadu a matsayin Manzo".
Explanation
Na farko: Ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, hakan ƙirjinsa ya buɗe ga abinda zai zo masa daga Allah da hukuncin Rububiyyah na raba arzuƙa da halaye, ba zai samu bijirewa ba a cikin zuciyarsa akan wani abu daga hakan, kuma bai nemi wani Ubangiji wanin Allah - Maɗaukakin sarki ba.
Na biyu: Ya yarda da musulunci a matsayin addini, hakan shi ne ƙirjinsa ya buɗe ga abinda musulunci ya ƙunsa na takalif da wajibai, bai tafi zuwa wanin hanyar Musulunci ba.
Na uku: Ya yarda da (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Manzo, hakan shi ne ƙirjinsa ya buɗe kuma ya yi farin ciki da dukkan abinda ya zo da shi ba tare da wani kaikawo ko kokwanto ba, bai shiga (wata hanya ba) sai abinda ya dace da shiriyar Manzonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Benefits
Jiki ba ya samun zaƙin abinci da abin sha sai a lokacin lafiyarsa, to haka nan zuciya idan ta kuɓuta daga cututtukan soye-soyen zuciya masu ɓatarwa da sha'awowi ababen haramtawa, to ya samu zaƙin imani, a duk lokacin da ya samu rashin lafiya da masassara ba zai samu zaƙin imani ba, kai zai iya jin zaƙin abinda a cikinsa akwai halakarsa da son zuciya da saɓo.
Mutum idan ya yarda da wani al'amari kuma ya so shi to al'amarinsa zai yi sauƙi gare shi, wani abu daga gare shi ba zai yi masa wahala ba, kuma ya yi farin ciki da dukkan abinda ya zo da shi, kuma zuciyarsa ta cakuɗa da walwalarsa, to haka nan mumini idan imani ya shiga zuciyarsa, to sai biyayyar Ubangijinsa ta sauƙaƙa gareshi kuma ransa ya ji daɗi gareta, wahalhalunta ba zasu wahalar da shi ba.
Ibunl-Kayim ya ce: Wannan Hadisin ya ƙunshi yarda da RububiyyarSa - tsarki ya tabbatar maSa da UluhiyyarSa, da yarda da ManzonSa da jawuwa gareShi, da yarda da addininSa da miƙa wuya gare shi.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

