Lallai abin da kake faɗa kuma kake kira zuwa gareshi mai kyau ne, ina ma dai ka sanar da mu cewa akwai kaffara ga abin da muka aikata
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - Lallai wasu mutane daga mushrikai, sun kasance sun yi kisa sun yawaita, sun yi zina sun yawaita, sai suka zo wa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai suka ce: Lallai abin da kake faɗa kuma kake kira zuwa gareshi mai kyau ne, ina ma dai ka sanar da mu cewa akwai kaffara ga abin da muka aikata, sai (faɗin Allah) ya sauka: {Waɗanda ba sa kiran wani ubangiji tare da Allah, kuma ba sa kashe rai wanda Allah Ya haramta face da haƙƙi, kuma ba sa yin zina} [Al-Furqan: 68], kuma (wannan ayar) ta sauka: {Kace: (Allah Ya ce), "Ya ku bayiNa waɗanda suka yi ɓarna a kan rayukanku! kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah} [Al-Zumar: 53].
Explanation
Sai ayoyi biyu suka sauka: Yayin da Allah Ya karɓi tuba daga mutane tare da yawan zunubansu da girmansu, da ba don haka ba, da sun zarce a kan kafircinsu da shisshiginsu da kuma ba su shiga wannan addinin ba.
Benefits
Yalwar rahamar Allah ga bayinSa da gafararSa da rangwaminSa.
Haramcin shirka, da haramcin kashe rai ba tare da wani haƙƙi ba, da haramcin zina, da narko a kan wanda ya aikata waɗannan zunuban.
Tuba na gaskiya abin wanda ya hadu da ikhlasi da aiki na gari yana kankare dukkanin manyan zunubai har ma da kafircewa Allah - Maɗaukakin sarki -.
Haramcin yanke ƙauna daga rahamar Allah - tsarki ya tabbatar maSa -.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

