Lallai cewa Allah zai tseratar da wani mutum daga al'ummata agaban halittu a ranar Alkiyama
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abdullahi dan Amr dan Al-Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa Allah zai tseratar da wani mutum daga al'ummata agaban halittu a ranar Alkiyama, sai Ya bude masa fayil dinsa x asa'in da tara, kowanne fayil tamkar iya ganinka ne, sannan Ya ce: Shin kana musun wani abu daga wannan? Shin marubutaNa masu kiyayewa sun zalinceka ne? Sai ya ce: A'a ya Ubangiji, sai Ya ce: Shin kana da wani hanzari? Sai ya ce: A'a ya Ubangiji, sai (Ubangiji) Ya ce: Eh, lallai kanada wani abu kyakkyawa a wurinmu, a yau babu wani zalinci akanka, sai a fitar da wani kati a cikinsa akwai: Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah , kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, sai ya ce: ka zo wajan ma'aninka, sai ya ce; ya Ubangiji wannan wanne katine tare da wadannan fayilillikan? Sai Ya ce; Lallai cewa kai ba za’a zalinceka ba, sai ya ce: Sai a dora fayilillikan a bangaren ma'auni , katin kuma a daya ma'aunin, sai fayililliakn su yi sauki, kuma katin ya yi nauyi, wani abu ba zai yi nauyi tare da sunan Allah ba".
Explanation
Benefits
Fadin: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ba ya isa da harshe kadai, babu makawa sai an san ma'anarta da kuma aiki da abinda take hukuntawa take nema.
Ikhlasi da karfin Tauhidi sababi ne na kankare zunubai.
Imani yana fifita da fififtar abinda ke cikin zukata na Ikhlasi, wani daga mutane zai iya fadin wannan kalmar saidai za'a yi masa azaba da gwargwadan zunubansa.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

