Wanda ya rantse sai ya ce a cikin rantsuwarsa: Na rantse da Lata da Uzza, to ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wanda ya ce wa abokinsa: Zo mu yi caca tare, to ya yi sadaka
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya rantse sai ya ce a cikin rantsuwarsa: Na rantse da Lata da Uzza, to ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wanda ya ce wa abokinsa: Zo mu yi caca tare, to ya yi sadaka".
Explanation
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labarin cewa wanda ya ce wa abokinsa: Zo mu yi wasan caca, - ita ce mutum ko sama da haka su yi rinjayeyeniya akan wata dukiyar da wani zai ɗauka a tsakaninsu, kuma kowanne daya daga cikinsu ba ya zama haka kodai yaci riba a cikinta ko kuma ya faɗi -; to an so ya yi sadaka da wani abu dan kaffara daga abinda ya yi kira zuwa gare shi.
Benefits
Rantsuwa da wanin Allah - Maɗaukakin sarki - haramun ce, daidai ne rantsuwace da gumaka kamar Lata da Uzza, ko rantsuwa da amana, ko rantsuwa da Annabi ko wanin hakan.
AlKhaɗɗabi ya ce: Rantsuwa kawai tana kasancewa ne da abin da ake bautawa abin girmamawa, idan ya yi rantsuwa da Lata da makacinsa to haƙiƙa ya yi kama da kafirai, sai aka umarce shi ya riski abinda ya fada da kalmar Tauhidi.
Babu kaffarar rantsuwa akan wanda ya yi rantsuwa da wanin Allah, kawai ya wajaba akan shi ya koma ga Allah da neman gafara; domin ta wuce ayi mata kaffara sai dai tuba.
Haramcin caca da dukkan surorinta da yanayinta, itace cacar da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya haramta kuma Ya haɗata da giya da gumaka.
Wajabcin barin saɓo a lokacin aikata shi .
Wanda ya afka a cikin wani mummunan abu to ya wajaba akansa ya bi shi da kyakkyawa; domin kyawawan ayyuka suna tafiyar da munanan ayyuka.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

