Shin bana shiryar daku ga mafi alheri daga abinda kuka tambaya ba? idan kun kwanta - ko kunzo shinfiɗarku - to ku yi tasbihi sau talatin da uku, ku yi hamdala sau talatin da uku, ku yi kabbara sau talatin da da hudu, to shi ne mafi alheri gareku daga dan aiki
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Faɗima - Allah Ya yarda da ita - ta zo wajen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - tana kawo ƙarar abinda take gamuwa da shi a hannunta na daka, kuma labari ya isar mata cewa wani bawa ya zo masa, bata same shi ba, sai ta ambaci hakan ga A'isha, lokacin da ya dawo sai A'isha ta ba shi labari, (Aliyu) ya ce: Sai ya zo mana alhali mun kwanta, sai muka tafi muka tashi, sai ya ce: "Ku zauna a wurinku" sai ya zo sai ya zauna tsakani na da ita, sai naji sanyin diga-digansa akan cikina, sai ya ce: "Shin bana shiryar daku ga mafi alheri daga abinda kuka tambaya ba? idan kun kwanta - ko kunzo shinfiɗarku - to ku yi tasbihi sau talatin da uku, ku yi hamdala sau talatin da uku, ku yi kabbara sau talatin da da hudu, to shi ne mafi alheri gareku daga dan aiki".
Explanation
Benefits
Wannan zikirin ba'a faɗarsa sai a baccin dare kawai, kuma lafazinsa a wurin Muslim daga riwayar Mu'azu daga Shu'uba "Idan kuka kwanta da daddare".
Idan musulmi ya manta wannan zikirin a farkon dare sannan ya tina shi a ƙarshensa to babu laifi; domin cewa Aliyu - Allah Ya yarda da shi - maruwaicin hadisin yana cewa shi ya manta faɗarsa a daren Siffin a farkon daren sai ya tina sai ya faɗeshi kafin Asuba.
Mihlab ya ce; A cikinsa akwai cewa mutum ya ɗora iyalansa kan abinda ya ɗora kansa aikai na fifita lahira akan duniya idan sun kasance suna da iko akan hakan.
Ibnu Hajar al’Asƙalani ya ce: Wanda ya lazimce shi ba zai cutu da yawan aiki ba kuma ba zai wahalar da shi ba koda gajiya ta faru gare shi.
Al’Aini ya ce: Ta fuskar alherin kodai ana nufin shi yana rataye da lahira ne shi kuma ɗan aiki da duniya, lahira kuwa ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa, ko kuma ana nufin dangane da abinda ta nema da cewa ikon da zata samu ya zama shi ne mafi karfi akan aikin da dan aiki zai yi mata.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

