Kada ku zagi Iska, idan kuka ga abinda ba kwa so to kuce: Ya Allah mu muna roƙonKa daga alherin wannan iskar, da alherin abinda ke cikinta, da alherin abinda aka umarce ta da shi, kuma muna neman tsarinKa daga sharrin wannan iskar, da kuma sharrin abinda ke cikinta, da kuma sharrin abinda aka umarce ta da shi
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku zagi Iska, idan kuka ga abinda ba kwa so to kuce: Ya Allah mu muna roƙonKa daga alherin wannan iskar, da alherin abinda ke cikinta, da alherin abinda aka umarce ta da shi, kuma muna neman tsarinKa daga sharrin wannan iskar, da kuma sharrin abinda ke cikinta, da kuma sharrin abinda aka umarce ta da shi".
Explanation
Benefits
Komawa zuwa ga Allah da neman tsari da Shi daga sharrin abinda Ya halitta.
Iska tana kasancewa abar umarta da alheri, kuma tana kasancewa abar umarta da sharri.
Ibnu Baaz ya ce: Zagin iska yana daga jumlar saɓo; domin ita abar halitta ce abar jujjuya al'amuranta ne, ana aikota da alheri da kuma sharri; saboda haka zaginta ba ya halatta, kuma ba'a cewa: Allah Ya tsinewa iska, ko Allah Ya kashe iska, ko kada Allah Ya yi albarka a cikin wannan iskar, ko abinda ke kama da haka, kai mumini ya yi aiki da abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Ana ƙiyasta abinda ya rataya da zafi da sanyi da rana da ƙura da wanin hakan daga abinda yake shi daga halittar Allah ne da tasarrufinSa, akan iska a cikin haramcin zagi da cin mutunci.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

