Ba ya kamata ga wani mutum musulmi da yake da wani abinda zai yi wasiyya da shi, ya kwana darare uku sai wasiyyarsa tana rubuce a wurinsa
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ba ya kamata ga wani mutum musulmi da yake da wani abinda zai yi wasiyya da shi, ya kwana darare uku sai wasiyyarsa tana rubuce a wurinsa", Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: "Wani dare bai taɓa wucewa gareni ba tunda na ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya faɗi haka ba sai wasiyyata tana tare da ni".
Explanation
Benefits
Wasiyya: Ma'anarta, ita ce mutum ya alƙwarantawa wani mutum yin tasarrufin wani abu daga dukiyarsa bayan mutuwarsa, ko ya alƙawarantawa wani mutum kan ya kula da 'ya'yansa ƙanana, ko ya alƙawarantawa wani mutum a wani abu daga ayyukan da zai mallakesu bayan mutuwarsa.
Wasiyya ta rabu gida uku: 1- Mustabbi, ita ce wasicci da wani abu daga dukiyarsa da za'a bada ita a tafarkin alheri, da kyautatawa; dan ladansa ya sadu da shi bayan mutuwarsa. 2- Ta wajibi, ita ce wasicci da abinda ke kansa na haƙƙoƙi, daidai ne sun kasance haƙƙoƙin Allah ne - Maɗaukaki sarki -, kamar zakkar da ba'a fitar da ita ba, ko kaffara, da makamancinsu daga abinda yake wajaba a asalin shari'a, ko waɗannan haƙƙoƙin sun kasance na 'yan Adam ne; kamar bashi, da maida amanoni. 3- wasiyyar da aka haramta, idan ta ƙaru akan sulusi (ɗaya bisa uku) daga dukiyarsa, ko idan ya yi wasicci ga wani mai gado.
Falalar Ɗan Umar - Allah ya yarada da su -, da gaggawarsa zuwa aikata alheri, da bin Mai shara'antawa Mai hikima.
Ibnu Daƙiƙul Id ya ce: Yin rangwami a cikin darare biyu ko uku dan kawar da ƙunci ne da kuma wahala.
Abubuwa masu muhimmanci yana kamata a kiyayesu da yin rubutu; domin cewa hakan zai fi sasu tabbatuwa kuma zai fi sa wa a kiyaye haƙƙoƙi.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

